Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Sibil Difens NSCDC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’an ta sun kama wani ƙasurgumin mai safarar makamai ɗauke da harsasai da dama sannan da wasu mutum bakwai masu haƙo ma’adinai ba tare da izini ba.
Shugaban rundunar Nuhu Muhammadu ya sanar da haka a garin Kaduna ranar Laraba.
“Jami’an rundunar a ranar Talatan yayin da suke sintiri a hanyar Mage road dake Tudun-Wadan Zaria suka kama ɗan achaɓa ɗaya da wani mutum.
“Yayin da suke gudanar da bincike a kansu ɗaya daga cikin mutanen sai ya gudu. ɗayan da suke tare mai suna Auwalu Ahmed mai shekaru 62 jami’an tsaron suka kama shi kuma sun sami tulin harsasai 440 a hannunsa.
“Jami’an tsaron na gudanar da bincike domin kamo abokin tafiyarsa da ya arce da sauran abokanan harƙallarsu.
“Da zaran an kammala bincike za a kai Ahmed kotu domin yanke masa hukunci.
Bayan haka Muhammadu ya ce jami’an tsaron a ranar 30 ga Satumba sun kama wasu mutane bakwai da laifin haƙo ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a ƙaramar hukumar Kachia.
“Tun bayan da na karɓi shugabancin wannan rundunar nake gargaɗin masu aikata laifi su shiga taitayinsu. Yanzu za su gamu ba rashin mutunci.
“Ina kira ga mutane da su ci gaba da mara mana baya domin tabbatar da tsaro a faɗin jihar.
Muhammadu ya miƙa godiyarsa ga shugaban rundunar NSCDC na ƙasa Ahmed Audi da gwamnan Kaduna Uba Sanibisa goyon baya da suke ba su a jihar.
