Daga UMAR GARBA a Katsina
Mazauna jihar Katsina musamman matasa waɗanda kan shirya tarurruka don murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai, sun ƙaurace wa shirya irin waɗannan shagulgula da su kan shirya a ranar 1 ga watan Oktoba na kowace shekara.
A bisa al’ada matasa, samari da ‘yan mata kan haɗu a wuraren shirya tarurruka sanye da tufafi iri ɗaya, galibi masu launin tutar ƙasar nan, ba don nishaɗantar da kansu ba kawai har ma da gudanar da jawabai da suka shafi cigaban ƙasar nan ko akasin haka.
Matasan kan yi amfani da ranar don sanar da shugabanni matsalolinsu waɗanda suka haɗa da rashin samun ingantaccen ilimi, rashin aikin yi da dai sauran buƙatansu.
To sai dai a wannan karon Blueprint Manhaja ta zagaya cikin birnin Katsina wuraren da ake shirya waɗannan tarurruka ba tare da ganin matashi ko ɗaya ba a wurin.
Kazalika, mazauna jihar sun ƙaurace wa zanga zangar da aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta wadda aka shirya yi a ranar 1 ga watan Oktoba na wannan shekarar, bayan zanga zangar tsadar rayuwa da aka yi cikin watan Ogasta da ya gabata.
A yayin da ma’aikata suka kasance a gida saboda hutun da gwamnatin tarayya ta bayar, su kuwa ‘yan kasuwa sun ci gaba da harkokin kasuwanci, gami da zirga zirgar ababen hawa a kan manyan titunan jihar.
Sai dai an ga jami’an tsaro na bada kariya ga wasu muhimman wurare, tun da farko jami’an ‘yan sanda a jihar sun ce, za su baiwa masu zanga-zangar ta ranar samun ‘yancin kai kariya don kare sake faruwar asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata.
Tun da farko wasu matasa sun yi rubuce-rubuce a shafukan soshiyal midiya inda suka bayyana cewar ba za su yi wani shagali ba a ranar samun ‘yancin kan ƙasar nan na shekarar 2024, kamar yadda suka yi a shekarun baya saboda dalilai masu cin karo da juna da suka kafa hujja da su.
Blueprint Manhaja ta tattauna da Mustapha Sani Abdullahi, matashin ɗan siyasa kuma mai amfani da shafukan sada zumunta, a cewar Abdullahi, matasa sun ƙaurace wa shirya bukukuwan murnar samun ‘yancin kai a wannan shekarar saboda matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa da ake ciki.
“Babban abin da ya sa matasa ba su iya shirya shagulgulan murnar samun ‘yancin kai ba kamar yadda aka saba a kowace shekara shine, da yawan matasan nan ma su yin wannan bukukuwa ‘ya’yan talakawa ne waɗanda sune ke nema wa kansu kuɗin buƙatatunsu na yau da kullum, yawanci masu sana’o’in hannu ne to yanzu irin waɗannan sana’o’in na hannu an durƙusar da masu yin su saboda yanayin da muke ciki na matsin tattalin arziƙi da kuma tsadar rayuwa sannan, ‘yancin da ake murna an samu kamar bai samu ba domin rayuwar da aka yi a baya tafi ta yanzu sauƙi,” inji matashin.
Kazalika wata matashiyar, Bilkisu Yunus ta bayyana wa wakilin jaridar Blueprint Manhaja cewa, rashin isassun kuɗi a hannun matasa ne ya hana su shirya tarurrukan murnar ranar samun ‘yancin kai.
“A shekarun baya muna da ‘yan kuɗin da muke ware wa saboda wannan hidimar, mu ke saya wa kan mu riguna,muke karɓar hayar ɗakin taro, a ɗauko MC da mawaƙa da za su nishaɗantar da mahalarta taro.
“Sannan mukan bayar da kyaututtuka ga matasa da suka yi fice a fannonin rayuwa daban-daban sai kuma ɗaukar nauyin manyan baƙi da za su gabatar da jawabi kan muhimmancin ‘National day’ to yanzu kowa ta kansa ya ke yi,” inji ta.
A na shi ra’ayin Abdul’aziz Abdulkarim, shugaban wata ƙungiya dake fafutukar nema wa matasa sana’o’in dogaro da kai, ya bayyana cewa bai kamata matasa su watsar da irin waɗannan bukukuwa ba duk da ƙasar na fama da ƙalubale daban daban, a cewar shi sauran ƙasashen duniya na nuna tsananin kishin ƙasa idan ranar samun ‘yancin kansu ta zagayo.
“Ina kira ga gwamnati da masu hali daga cikin al’umma akan su samarwa matasa abun yi saboda rashin aikin yi ko sana’a na haifar da rashin kishin ƙasa a tsakanin matasa .” Inji shi.
Saboda haka ana iya cewa gwamnatin jihar Katsina da wasu ɗai ɗai kun mutane ne a jihar suka samu damar shirya irin wannan taro ko biki na taya ƙasar nan murnar cika shekara 64 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin ƙasar Birtaniya.
Albarkacin ranar, a jawabin da gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya gabatar ya yi kira ga shugabanni akan su ƙara zage dantse wajen kawo wa al’umarsu cigaba daga nan sai ya buƙaci ƙabilun ƙasar nan da su haɗa kawunansu don ɗorewar zaman lafiya gami da ci gaban ƙasarmu Nijeriya.
