
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’an tsaro na farar hula (Civil Defence) a katsina sun kama mutum uku bisa zargin su da satar wayar wutar lantarki mai amfani da hasken rana.
A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar, DSC Buhari Hamisu ya bayyana cewa cikin waɗanda ake zargin akwai Hassan Sulaiman da Jamaluddeen waɗanda ke zaune a cikin garin Katsina.
DSC Buhari ya kara da cewa, hukumar ta samu nasarar kama waɗannan matasan ne a titin Usman Nagode kusa da tsohuwar ma’aikatar ayyuka inda suka aikata laifin.
Su dai waɗannan matasa da jami’an suka kama, hakan ya faru ne bayan da suka cire fitillun da ke kan hayar babban titin da kuma amfani da sigar da zargi wajen cire rodunan da ke haɗe da sandunar wutar lantarkin.
Ɗaya daga cikin mai taimaka wa maɓarnatan, Mubarak Dan-Kaita, a halin yanzu ana neman sa ruwa a jallo.
Sanarwar ta ce rundunar tsaron ta kama wani matashin mai suna Aliyu Yunusa mazaunin Ƙofar sauri a Katsina wanda shima ya aikata irin laifin.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar ya ƙara da cewa binciken da hukumar ta yi, ya gano cewa waɗanda matasa na bin manyan hanyoyin cikin garin Katsina su na cire fiitilun kan hanyar da tunɓuke rodukan sandunan wutar lantarkin.
Ƙarafunan da suke amfani da su sun haɗa da zarto, babban ƙarfe da keke NAPEP da ke ɗaukan kayan satar.
Bayanin ya kuma nuna cewa, da zarar hukuma ta kammala bincike za a tura su gaban ƙuliya.
Kazalika, ya jaddada ƙudirin hukumar na tabbatar da tsaro ga al’ummar jihar da kuma kadarorin gwamnati.
