Za a ƙara mu’amala da koyi da juna tsakanin ƙasashen Sin da Afirka 

Spread the love

Daga: LI HONGFENG

(Shugabar Kwalejin Nazarin Nahiyar Afirkan BFSU)

A ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2023, yayin da babban sakataren jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin ɗi Jinping yake gabatar da jawabi a yayin taron tattaunawa tsakanin jam’iyyar kwaminisancin ƙasar Sin (JKS) da sauran manyan jami’o’in ƙasashen duniya, ya gabatar da shawara kan raya wayewar kai ta duniya. An bayyana wannan shawara a ƙarƙashin fahimtar ƙasar Sin game da wayewar kai da mu’amala a tsakanin ƙasashen duniya. Yayin da ake ƙoƙarta wajen aiwatar da wannan shawara, mu’amala da koyi da juna game da wayewar kai tsakanin ƙasashen Sin da Afirka ya riga ya zama wani babban ginshiƙi, wanda ya kafa misali ga mu’amala a ƙasashen duniya.

Tun fil azal, akwai mu’amala sosai a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, akwai rubuce-rubuce game da mu’amala a tsakaninsu tun daga daular Tang. Tun bayan da ƙasashen Afirka suka samu ’yancin kai, haɗin gwiwar moriyar juna cikin daidaito tsakanin Sin da Afirka ya nuna fahimtar ɓangarorin biyu game da raya mabambantan al’adu a duniya. Sin da ƙasashen Afirka suna da ra’ayin fahimtar duniya kusan irin ɗaya a tsakaninsu, kuma sun yi na’am da haɗin gwiwa cikin jituwa. ƙasashen Afirka sun nace kan tafarkin raya haɗin gwiwa ta ɓangarorin daban daban, da zaɓar hanyar samun bunkasuwa da kansu, wannan ya nuna ’yancin kan tunanin samun bunƙasuwar ƙasashen Afirka, kuma wannan ya dace da wayewar kan ƙasar Sin.

Wayewar kan ƙasashen duniya na bukatar koyi da juna tsakanin wayewar kan Sin da Afirka, kuma aka nuna adawa ga nuna bijirewa ga sauransu. Wayewar kan duniya ya mai da hankali kan gadon abubuwan tarihi da ƙirƙiro da sabbin abubuwa don yin koyi da juna tsakanin wayewar kan ƙasar Sin da ƙasashen Afirka. A ƙarƙashin nagartattun halayye, aka ƙirƙiro da sabbin abubuwa a fannin al’adu. Shehun malamin Senegal Cheikh Anta Diop ya bayyana cewa, duk wanda ke iya samun bunƙasuwa da kansu a cikin tarihi, za su iya samar da yanayin da ake bukata wajen buƙasuwa, kuma ana bukatar ƙirƙiro da sabbin abubuwa a wannan fanni.

Shawarar da aka gabatar game da koyi da juna a fannin al’adu, ya samar da sabuwar hanya ga musayar al’adu a tsakanin ƙasashen Sin da Afirka. ƙasashen Sin da Afirka za su yi koyi da juna a fannin ra’ayin fahimtar duniya, don samu haɗin gwiwa game da samu ra’ayi guda, da raya kan shawarwai tsakanin mabambantan wayewar kan duniya. A sa’i ɗaya kuma, ƙasashen Sin da Afirka na bukatar ƙara haɗin gwiwa a fannin al’adu. A matsayin muhimmiyar abokiyar haɗin gwiwa bisa manyan tsare-tsare ta ƙasashen Afirka, ƙasar Sin ta nuna goyon baya game da ƙasashen Afirka a fannonin manyan ababen more rayuwa da gina abubuwan gado da aka gada daga kaka da kakanni, da gudanar da ayyukan al’adu. Nan gaba, za su iya ƙara inganta haɗin gwiwa a fannin horar da ƙwararru a fannin al’adu da horar da fasahohi, da more fasahohin da aka samu wajen tafiyar da harkoki. Ban da wannan kuma, akwai makoma sosai game da mu’amala a tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka, za su kyautata mabambantan al’adu, don samar da daidaito a tsakain yankunan daban daban, da kyautata dangantakar Sin da Afirka a tsakaninsu.

Yanzu, rikicin da yaƙi-ci-yaƙin-cinyewa ke ci gaba da kawo lahani ga zaman lafiya cikin jituwa a duniya. An gabatar da shawara game da wayewar kan duniya bisa tarihi da yanayin da ake ciki yanzu, don nuna girmama ga wayewar kan duniya, da inganta samar da ra’ayin ɗan Adam a duniya, da mayar da hankali kan gadon wayewar kai, da inganta haɗin gwiwa da mu’amala a ƙasashen duniya, don kawar da saɓani da ƙiyayya a ƙasashen duniya, ta hakan, za a ƙara cusa sabbin abubuwa game da koyi da juna a tsakanin wayewar kan ƙasashen Sin da Afirka. ɓangarorin biyu za su more fasahohin da aka samu, don samun ci gaba tare.

By ukarofi