MDD ta koka kan rashin warware rikicin siyasar Libya

Spread the love

Majalisar Ɗinkin Duniya ta koka da yadda ƙoƙarin warware rikicin siyasar Libya ke ci gaba da ganin tarnaƙi lura da yadda ake ganin koma baya a dukkanin yunƙurin da ake na samar da fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da ke mulkin ƙasar.

Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya a Libya, Taher Al-Sunni ya shaidawa zaman kwamitin tsaro na majalisar cewa halin da ake ciki a ƙasar na matuƙar ɗaure kai musamman a watanni biyun da suka gabata, ta yadda ake ganin farraƙa a dukkanin ɓangarorin da suka shafi siyasa tattalin arziki da ma yunƙurin tabbatar da tsaro a ƙasar ta yankin Magreb a nahiyar Afrika.

A cewar Al-Sunni halin da ake ciki a ƙasar ya sanya shakku a fatan da ake da shi na cimma jituwa tsakanin ɓangarorin da ke mulkin ƙasar a Tripoli da Benghazi.

Cikin watanni biyu da suka gabata, an samu ɓaraka mai girma tsakanin ɓangarorin biyu wadda ke ci gaba da tsananta kama daga fannonin siyasar tattalin arziki da kuma tsaro lamarin da ya yi mi’ara koma baya ga yunƙuri ƙasashe na samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasar wadda ta shafe tsawon shekaru ta na fuskantar yaƙin basasa.

Taher Al-Sunni ya shaidawa kwamitin cewa hanya ɗaya ta warware rikicin Libya bai wuce gudanar da sahihin zaɓe ba.

Rikicin baya-bayan nan da ɓangarorin biyu suka samu farraƙa akai shi ne korar gwamnan babban bankin ƙasar Sadiƙ al-Kabir da gwamnatin Tripoli ta yi da nufin maye gurbinsa da wani ko da ya ke an bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓawa doka.

Libya ta faɗa yaƙin basasa ne tun bayan da NATO ta jagoranci tawagar Sojin ƙasashe wajen yaƙar Moammar Gadhafi a shekarar 2011, shugaba mafi daɗewa a kujerar mulki a tarihin ƙasar.

By ukarofi