
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗansa, Wale Tinubu wanda shi ne shugaban Kamfanin Oando, ba su da ra’ayin sayan kamfanin ‘OVH Energy’.
Hakan na zuwa ne bayan da tsohon Mataimakin shugaban, Alhaji Atiku Abubakar ya ce wasu ƴan ɓangaren Tinubu ne suka ƙwace kamfanin.
Cikin wata sanarwa da Mai bashi Shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, Atiku ya bayyana yadda NNPC ta sanya wani reshenta a ƙarƙashin hukumar gudanarwar OVH wanda Oando ya mallaki kaso 49 na hannun jari acikin sa.
Atiku ya bayyana hakan a matsayin wani salo na ƙoƙarin mallake NNPC daga ƴan ɓangaren Tinubu ta hanyar amfani da ƙarfa-ƙarfa, ya na mai cewa yin hakan fashi ne daga gare su.
Saidai yayin da NNPC ke mayar da martani game da batun, ya ce maganar Atikun ba gaskiya ne, ya na mai cewa Shugaba Tinubu ko ɗansa Wale ba su da wani ra’ayi na mallakar kamfanin, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na NNPC, Olufemi Soneye ya faɗa acikin wani jawabi da ya fitar.
Ya ce, kamfanin a na gudanar da shi ne ƙarƙashin kulawar ƙwararru da suke ƙoƙarin ƙara wa Najeriya daraja inda ya ce hukumar gudanarwa ta NNPC ta na la’akari da inda za ta zuba hannun-jari da kuma maslahar ƙasa.
