Jami’an tsaro sun kama Bello Baɗejo a Jalingo bayan bayyana muradin tsaya wa takarar sanata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, sun kama Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Baɗejo jim-kaɗan bayan ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar sanata a mazaɓar Taraba ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An kama Baɗejo ne a birnin Jalingo, Babban Birnin Jihar Taraba.

Bayanan sun nuna cewa Baɗejo ya isa filin jirgin sama na Ɗanbaba Suntai da ke garin Jalingo cikin jirgi mai zaman kansa, inda dubban magoya baya suka tarbe shi daga ƙananan hukumomin mazaɓar.

An ruwaito cewa, an kama shi ne da dare bayan ya kai ziyara wasu hukumomin tsaro tare da abokan siyasarsa, jim-kaɗan bayan ganawa da magoya bayansa a sakatariyar APC ta Taraba.

Wani mai taimaka masa mai suna Umar, ya ce jami’an tsaron da suka raka shi daga Abuja zuwa Jalingo su ne daga bisani suka kama shi, inda har yanzu ba a san inda aka tsare shi ko dalilin kama shi ba.

Gabanin kamen, Baɗejo ya bayyana cewa ya sayi fom ɗin takarar sanata kuma ba zai janye wa kowane ɗan takara ba duk da matsin lamba daga wasu ɓangarori.

By Babaji