
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta sake ɗage sauraron ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage sauraron shari’ar ba tare da sanya wata sabuwar ranar cigaba da sauraro ba, bayan da lauyan mai ƙara ya sanar da kotun cewa sun rubuta wa Babban Alƙalin Kotun Tarayya wasiƙa domin neman a mayar da shari’ar gaban wani alƙali daban.
Mai ƙarar, Nafiu Bala Gombe, na ƙalubalantar wasu matakai da suka shafi shugabancin jam’iyyar ADC, inda yake neman kotu ta yi hukunci kan halaccin tsarin jagorancin da ake gudanarwa ƙarƙashin Sanata David Mark.
A zaman kotun na baya-bayan nan, lauyan mai ƙarar ya bayyana cewa buƙatar sauya alƙalin na da alaƙa da neman tabbatar da adalci da kuma kauce wa duk wani zargi na rashin gaskiya a shari’ar.
Sai dai lauyoyin waɗanda ake ƙara ba su nuna adawa kai tsaye da matakin neman sauya alƙalin ba, yayin da kotun ta yanke shawarar dakatar da ci gaba da sauraron ƙarar har sai an yanke hukunci kan buƙatar da aka miƙa wa Babban Alƙalin Kotun Tarayya.
Rikicin shugabancin ADC ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar a ‘yan kwanakin nan, musamman bayan sauye-sauyen shugabanci da suka haɗa da fitowar wasu manyan jiga-jigai domin jagorantar tafiyar jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
