Daga SAN AHMAD GIWA a Abuja
Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ƙaddamar da kwamitin ƙaddamar da gidauniyar tallafa wa jami’ar bayan naɗa tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta ƙasa, Muhammad Babandede, a matsayin shugaban kwamitin.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Abbas Sagir, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin tare da roƙon mambobin kwamitin da su yi ƙoƙarin wajen ganin san samar wa da jami’ar abin da za ta yi amfani da shi wajen samar da cigaba mai ɗorewa ga masu zuwa nan gaba.
Shugaban jami’ar ya jaddada muhimmancin kafa gidauniyar wadda ake sa-rai za ta taimaka wajen samar da cigaba da makoma mai kyau ga jami’ar.
Ya ce wannan yunƙuri na zuwa ne domin samar da kuɗi da za a riƙa gudanar da bincike da kayan more rayuwa da duk wani abu da ai samar da cigaba ga jami’ar.
“Kwamitin ya ƙunshi manya-manyan mutane da suka yi aiki har a gwamnatin tarayya da ma ƙasashen waje kuma sun karɓi wannan aiki. Muna fatan za su aiwatar da shi yadda ya kamata,” Farfesa Sagir, shugaban jami’ar BUK.
Daga nan ya buƙaci a yi aiki da gaskiya wajen samar da kuɗi da buƙatar wayar da kan al’umma kan muhimmancin ba da tallafi.
A yayin da yake magana kan kafa wannan gidauniya, tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta ƙasa, Muhammad Babandede kuma shugaban gidauniyar, ya ce, “ana irin wannan gidauniya a kowacce babbar jami’a a duniya kuma abin ciwo ne yawancin jam’o’inmu na Arewa a nan ba mu da shi. Amma alhamdulillah, an yi sa’a an samu shugaban jami’ar mai kula, mai tunani da kuma shugaban tsofaffin ɗalibai waɗanda suka zauna aka kuma kafa gidauniyar.”
Sannan ya yi ƙarin haske game da kudin da ake sa ran gidauniyar za ta samar, inda ya ce, “tallafin gidauniyar za a yi amfani da shi ne wajen gudanar da bincike – bincike da zai taimaki al’umma. Ba ana tara kuɗin ba ne domin a yi biki ko kwalliya.”
Hakazalika, ya ce, ba a amfani da irin wannan kuɗi wajen biyan albashin malamai da gini ko gyaran gini ko ciyarwa da makamantansu. Daga nan ne yajaddada muhimmancin amfani da kuɗin wajen gudanar da bincike.
Shuaibu Idris Mikati, shi ne shugaban ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na Jami’ar (BUKAA) wanda ya ce wannan yunƙuri na kafa gidauniyar ya samo asali ne daga irin tunani na shugabancin ƙungiyar ta la’akari da irin ƙalubalen da jami’ar ke fuskanta kamar rashin tsayayyiyar wutar lantarki.
Kwamitin gidauniyar samar da tallafin ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane da suka haɗa da tsohon sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Hafizu Ringim da ambasada Aishatu Musa da JanarSani Kuka-sheka da Ahmad Usman Elmarzuƙ da Farida Dankaka da Hakama Sidi Ali da Dr. Bala Muhammad da Peter Esan da Usman Bala da sauransu.
