Jam’iyyar ADP ta nemi INEC ta yi bincike kan hotunan AI a jaddawalin rajistar masu zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar ta bayyana takaicinta kan yadda aka samu wasu rahotanni da ke nuna cewa akwai waɗansu kurakurai a cikin jaddawalin rajistar masu zaɓe da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar musamman kan zargin samun hutunan ƙirƙirar fasahar AI aciki.

A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Shugaban Jam’iyyar, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, ADP ta bayyana cewa wannan al’amari na buƙatar a gaggauta gudanar da bincike a kai tare da tabbatar da gaskiya da adalci yayin aiwatar da haka.

A cewarsa, kasancewar Daraktan yaɗa labaran INEC ya bayyana cewa wasu jami’an rajista sun shigar da hotunan AI acikin tsarin, hakan ya tayar da muhimman tambayoyi akan inganci da tsaron kayan aiki na harkokin hukumar musamman kan abin da ya shafi matakan daƙile maguɗin zaɓe, yana mai cewa muddin aka samu gazawar gyara kurakuran hakan ka iya karya ƙwarin-gwiwar da jama’a ke da shi akan hukumar.

Akan haka ne jam’iyyar ta kirayi INEC da ta hanzarta gudanar da aiki akan gano hotunan na fasahar, gano rajistar da aka ƙirƙira, rahotannin da suka bayyana sau biyu da wasu kurakurai da ake zargin akwai aciki yayin ƙoƙarin tabbatar da tsare gaskiya da adalci.

ADP ta kuma buƙaci hukumar da ta samar wa jam’iyyun siyasa ingantattun bayanai akan kurakuran da aka samu, matakan gyaran da aka ɗauka da kuma ababen da aka samar don kare sake aukuwar ire-iren matsalolin a nan gaba, tana mai cewa akwai buƙatar a yi amfani da kayayyakin fasaha bisa tsarin da doka ta tanada ta yadda za a gamsa da dukkan masu ruwa da tsaki kan sahihancin ayyukan hukumar.

Sannan, ta shawarci INEC da ta ƙarfafa lamuran shawarwari da jam’iyyu, ƙungiyoyin al’umma, masu sanya ido kan harkokin zaɓe da hukumomin tsaro domin ƙarfafa matakan tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin zaɓe da martaba tsarin dimukraɗiyya a Nijeriya a idon duniya.

By Babaji

Leave a Reply