Jam’iyyar Labour ta lashe zaɓen Ingila yayin da gwamnatin Conservative ta faɗi warwas

Spread the love

Jam’iyyar Labour tayi nasarar samun kujeru 326 a zaɓen Ingila, wanda hakan na nufin itace zata kafa gwamnati, wanda Keir Starmer zai zama Firayim minista.

Wanda Jam’iyyar ta conservative ta samu nasarar kujeru 58, wanda hakan na nufin, ta samu kaso 21.1% na zaɓen. Sai Liberal Democracy sun samu, kaso 10.6% na zaɓen, green party da SNP duk suma sun samu kaso kaɗan daga cikin zaɓen.

Ministoci takwas sun rasa kujerun su a wannan babban zaɓen, wanda haka ya karya tarihi da ake dashi na shekarar 1997 wanda ministoci bakwai suka rasa kujerun su. Tuni dai Firayim Minista na yanzu Rishi sunak ya karɓi sakamakon Faɗuwar.

By ukarofi