Gangamin yaƙin neman zaɓen Donald Trump da wasu daga cikin abokansa sun fara riga-kafin siyasa kan mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris, inda suka yi gaggawar ƙoqarin ɓata mata suna a yayin da wasu ‘yan jam’iyyar Democrats suka yi hasashen cewa za ta maye gurbin shugaban ƙasa Joe Biden a saman tikitin takarar shugaban ƙasa na 2024.
A shafukan sada zumunta da kuma wasu kalamai da aka yi ta yi a tsakanin awowi 48 da suka gabata, da alama yaƙin neman zaɓen Trump da ‘yan jam’iyyarsa na Republican suna shimfiɗa harsashin kai hari kan Harris idan Biden mai shekaru 81 ya yanke shawarar kawo ƙarshen sake zaɓensa.
Duk da cewa Biden ya dage kan ba zai bar takarar ba watanni huɗu kafin zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 5 ga watan Nuwamba, kuma Harris ta tsaya ƙyam a bayansa, wanda hakan ya sanya yaƙin neman zaben Trump a tunani, wanda ya ga dacewar fara kai wa mataimakiyar shugaban ƙasar hari a yanzu, duba da cewa idan har ta maye gurbin maigidanta, za ta fito ne a ƙuraren lokaci da zai iya raunana su.
Daɗaɗen abu ne sukar ‘yan Republican zuwa ga mataimakiyar shugaban ƙasa, Harris, a lokacin mulkin Biden, saidai hare-haren na wannan makon sun linka waɗanda aka saba yi, domin suna wakiltar wani ci gaba mai girma kuma da alama ana danganta shi da ƙaruwar magana game da yiwuwar maye gurbin Biden a matsayin ‘yar takarar shugaban ƙasa ta Democrat
.Kwamitin Majalisar Wakilan Republican na ƙasa, wanda ke sa ido kan tserin Republican na Majalisar, ya kira Biden ta “mai ba da iko a kan gaba.”MAGA Inc, babbar ƙungiyar PAC ce ta tara kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen Trump, ta fitar da wata sanarwa da ta kira ta “sarkin mamaya “
A cikin Maris 2021 Biden ya ce Harris za ta jagoranci haɗin gwiwa da Mexico da ƙasashen Amurka ta Tsakiya don magance kwararowar baƙin haure ba bisa qa’ida ba.’Yan jam’iyyar Republican sun yi amfani da wannan wurin aika suka ta gazawar mataimakiyar ta shugaban ƙasa, inda suke zarginta da gazawa wajen daƙile kwararar miliyoyin baƙin haure da ke tsallaka wa cikin Amurka ba bisa ƙa’ida ba, duk da cewa ba ta taɓa ɗaukar alhakin tabbatar da tsaron iyakar kudancin ƙasar ba.
“Mataimakiyar shugaban ƙasa mafi rauni, mafi muni a tarihi, kuma tana goyon bayan Joe Biden 100% a cikin kowacce irin mummunar manufa da ya aiwatar cikin shekaru hudu da suka gabata,” inji Karoline Leavitt, mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Trump.
Trump ya caccaki Harris a wani faifan bidiyo da aka naɗa a ɗaya daga cikin wuraren wasan golf, wanda jaridar Daily Beast ta buga ranar Laraba, yana mai cewa Harris “ba mutuniyar kirki ba ce, kuma abin tausayi ce,” kafin ya yi amfani da wata dabara wajen kwatanta ta.
Kamfen ɗin Trump ya tsaya kan kalamansa, tare da manajan yaƙin neman zaɓen Chris LaCivita yana cewa a kan X: “Babu wani abu da ke cikin wannan bidiyon da ba daidai ba.”Mai magana da yawun yakin neman zaɓen Biden, Sarafina Chitika ta ce, “A’a, Donald. Abin da ba shi da kyau shi ne kwace ‘yancin mata, abin da ba shi da kyau shi ne rasa zaɓe da kuma ƙarfafa gungun masu tayar da ƙayar baya su kai hari Capitol.
“Yaƙin neman zaɓen na Biden ya ja baya kan sukar da Republican ke yi na Harris ba tare da yin la’akari da tambayar ko mataimakin shugaban ƙasa na jiraye da abinda suke zargi.
Rhyan Lake, mai magana da yawun kamfen na Harris ya ce “Mataimakiyar Shugaban ƙasa Harris na alfahari da kasancewa abokiyar takarar Shugaba Biden. Duk irin harin ƙarya da Trump da manyan abokansa suka yi, za ta ci gaba da kare tarihin Biden-Harris tare da ci gaba da gabatar da Donald Trump a gaban kuliya.”
Wannan zage-zage da Harris ke sha daga sansanin Trump da magoya bayansa bai kasance irinsa na farko da suka yi ba, asalima ya zama wata hanya da suke bi wurin raunana abokan hamayyar su, domin irin wannan hanya ce tsohon shugaban ƙasa Donald Trump, ya yi amfani da ita wajen yin nasarar lalata siyasar Ron DeSantis, babban abokin hamayyar sa na Republican, kafin gwamnan Florida ya tsallake rijiya da baya a zaɓen fidda gwani na jam’iyyarsu ta 2024 a bara.
Corey Lewandowski, wacce ta daɗe tana bai wa Trump shawara, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, Harris na da rauni a siyasance ganin irin rawar da ta taka wajen magance baƙin haure ba bisa qa’ida ba, da dai sauran batutuwan da ke cikin wani gagarumin bincike da jam’iyyar ta tattara kan tarihinta.
Masu kare Harris sun ce ta zama abin hari ne saboda rawar da ta taka wajen kai wa Trump hari kan haƙƙin zubar da ciki da kuma kakkausar murya da ta yi wa Biden a yaƙin neman zabe.Idan Biden zai fice daga takarar kafin taron ƙasa na Dimokraɗiya a watan Agusta, babu tabbacin Harris ce za ta zama wanda aka zaɓa. Amma a matsayinta na mataimakiyar shugaban ƙasa, mai yiwuwa ita ce za ta kasance ta farko a cikin layi. Za ta ci gajiyar babban yakin neman zaɓen Biden kuma da alama za ta iya ganin wani babban ɓangare na ‘yan Democrat sun mata mubaya’a a a ƙoƙarin gujewa faɗan jam’iyya mai zafi.
