Jarumi a Nollywood, Mr Ibu ya rasu yana da shekara 62

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa jarumi a masana’antar shirya finafinai ta Nollywood, John Okafor da aka fi sani da Mr Ibu, rasuwa.

Tashar Channels Television ce ta bayyana mutuwar jarumin a ranar Asabar.

Majiya ta kusa da marigayin ta shaida wa Channels Television cewa, a ranar Asabar da rana jarumin ya riga mu gidan gaskiya a wani asibitin Lekki da ke Legas.

Marigayin mai shekara 62, an garzaya da shi asibiti ne kusan mako guda da ya gabata sakamakon rashin lafiya.

A shekarar da ta gabata aka yi wa jarumin aiki inda aka cire masa ƙafa guda sakamakon lalurar rashin lafiyar da yake fama da ita.