Masarautar Jama’a ta naɗa wa ’ya’yanta huɗu sarautu

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan

Masarautan Jama’a da take Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna ta naɗa wa wasu ‘ya’yanta huɗu waɗanda suka cancanta sarautun gargajiya.

A lokacin da yake naɗa musu sarautun a fadarsa dake Kafanchan a ƙarshen mako, Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda aka yi wa naɗin ne saboda cancantarsu a bisa ƙoƙarin kawo ci gaban masarautan da suke yi.

A dalilin haka Sarkin ya yi kira da su ƙara hoɓɓasa bisa abinda suka saba yi saboda ciyar da masarautar gaba.

A nata jawabin, babbar baƙuwa a wajen bikin naɗin, mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe, ta taya waɗanda aka naɗa murna sa’annan ta shawarcesu da su yi amfani da sabbin muƙaman da aka ba su wajen taya Gwamnatin Jihar Kaduna a ƙoƙarin da take yi domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummanta.

Hajiya Sabuwa ta ƙara da cewa, su yi la’akari an zave su saboda cancanta saboda da haka sun shiga gurbin zavavvu da jama’a suna sa musu ido da begen za su bada cikakken gudummuwa wajen raya masarautarsu da Jihar Kaduna gaba ɗaya.

Waɗanda aka naɗa musu sarautun sun haɗa da: Abubakar Hassan (Dujaman Jama’a), Hayatu Labaran, (Sa’in Jama’a), Lawal M. Tanimu, (Mabuɗin Jama’a) da Alhaji Ibrahim Sani, (Kangiwan Jema’a).

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Abubakar Hassan (Dujaman Jama’a) a madadin waɗanda aka yi musu naɗi ya ce, sun karvi wannan nauyi da aka ɗora musu da hannu biyu.

Abubakar ya gode wa Mai martaba Sarkin Jama’a saboda ba su wannan damar bada tasu guddumuwa wajen raya masarautarsu. Ya ƙara da yin alƙawari cewa ba za su yi ƙasa a guiwa ba, amma za su karvi wannan ƙalubale ta hanyar ɗorawa bisa abubuwan ci gaba da aka sansu da su.