Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya bai wa ƙungiyar Izala mai shalkwata a Jos Naira miliyan goma don gudanar da harkokin tafsir na watan Ramadan da ke tafe.
Gwamnan ya bayyana bayar da wannan gudunmawar ne a lokacin gudanar wani babban taron shekara-shekara da ƙungiyar Izala da ke da shalkwata a Jos ke gudanarwa a lokacin karatowar azumin watan Ramadan wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a dake tsohuwar mayanka a cikin garin Birnin Kebbi babban birnin jihar.
Da yake jawabi a madadin Maigirma Gwamna, wakilin Gwamnan kuma Kwamishinan ayyuka na musamman Honorabul Zayyanu Umar Aleiro ya yaba wa ƙungiyar Izala Jos wajen ƙoƙarin da ta ke yi na yaɗa addinin Musulunci a cikin kwanciyar hankali da lumana.
Haka kuma ya bayyana cewa ayyukan ƙungiyar wajen yaɗa addinin Musulunci yana tasiri sosai wajen samar da kyawawan ɗabi’u tsakanin al’umma musamman a lokacin tafsirin watan Ramadan.
Haka kuma ya gode wa malaman addinin Musulunci a madadin Maigirma Gwamna akan irin haƙuri da juriya da suke nunawa wajen yaɗa addinin Allah inda ya buƙaci da su cigaba da kyawawan ayyukan da suke yi domin ci gaba da samar da zaman lafiya tsakanin al’umma.
A nasa jawabin shugaban ƙungiyar na jihar Kebbi, Sheikh Abdul Rahman Isah Jega ya yi godiya ta musamman ga maigirma Gwamna bisa irin kokarin da ya ke yi wajen kyautatawa al’ummar jihar domin sanya su farin ciki musamman irin kyautar ba-zata da ya ke yi wacce musulunci yana son irin ta.
Haka kuma ya yi kira ga maigirma Gwamna da ya cigaba da ayukan alheri da ya ke yi da kuma taimakon addinin Musulunci.
