Daga HABU ƊAN SARKI, Jos
A sakamakon yadda ake yawan samun tashe-tashen hankula da faɗan daba a tsakanin wasu gungun matasan Jos da suka faɗare suna ɗaukar makamai suna cutar da jama’a, musamman a lokacin bukukuwan sallah, ya sa shugabannnin al’ummar Jasawa ƙarƙashin haɗin gwiwar ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da jami’an tsaro na ýan banga, sun ɗaura ɗamarar ganin an kawar da duk wasu ɓatagari da ke kawo tashin hankali a cikin Jos da kewaye.
A wani zama na musamman da aka gudanar a babban masallacin Jumma’a na Jos, wakilan ɓangarorin al’ummar sun yi alwashin tabbatar da ganin an gudanar da shagulgulan babbar Sallah cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar ƙungiyoyin al’ummar gari, Alhaji Sani Mu’azu, Makaman Jos ta Arewa, kuma fitaccen jarumin finafinan Hausa da na turanci, ya buƙaci haɗin kai da aiki tare a tsakanin ɓangarorin, tare da tabbatar da cewa, duk wanda aka kama da laifin ɗaukar makami ko yunƙurin illata wani, da karya dokokin da gwamnatin Jihar Filato da rundunar ‘yansanda ta jihar suka gindaya, za a miƙa shi ne ga hukumomin da alhakin hukunta shi ya shafa, don su ɗauki matakin da ya dace a kansa.
Ya gargaɗi ýan banga da su guji hukunta waɗanda aka kama da laifi, ta yadda zai jikkata ko ya fita a hayyacinsa. Domin hukumar ƴansanda ce kaɗai doka ta amince su hukunta mai laifi.
Ya kuma yi kira ga masu babura da su yi biyayya ga dokar taƙaita zirga-zirga da gwamnati ta kafa, don kaucewa yaɗuwar fitina a cikin gari, da daƙile hanyoyin da ɓatagari ke bi suna aikata ɓarna da rashin tsaro.
Sakataren ƙungiyar cigaban al’ummar Jasawa, Malam Sani Suleiman Maigoro ya nemi ɓagarorin da za su gudanar da aikin sa ido da tsaro su zama masu kiyaye ƙa’idojin aiki, kuma su riƙa musanyar bayanai a tsakanin su, domin samun sauƙin sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya kamata.
