Jawabina ba shi da alaƙa da abinda ya faru a Ribas, tsohon tarihi na bayar – Shettima

Spread the love

Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana damuwa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka juya maganganun Sanata Kashim Shettima da ya gabatar a lokacin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da littafin “OPL 245: The Inside Story of the $1.3 Billion Oil Block” a Abuja, ranar Alhamis.

Sanarwar, wadda mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, ta bayyana cewa jawabin Shettima na nuni ne zuwa ga tsohon tarihin matsalolin da ya fuskanta a lokacin yana gwamna a Borno sakamakon rikicin Boko Haram, ba wai yana tsokaci ne kan abubuwan da ke faruwa a Jihar Ribas ba.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Shettima ya yi amfani da misalan tarihi ne don yaba wa marubucin littafin, Mohammed Bello Adoke (SAN), bisa jajircewarsa a lokacin da ya ke Ministan Shari’a na Ƙasa.

Ofishin ya ƙara da cewa, Shugaba Bola Tinubu bai tsige Gwamna Siminalayi Fubara daga mukaminsa ba, saidai an dakatar da shi bisa matakin doka domin dawo da doka da oda a Jihar Ribas.

An dauki matakin ne bisa tanadin Sashe na 305 na kundin tsarin mulki, tare da amincewar majalisar dokoki ta ƙasa.

A ƙarshe, Sanarwar ta bayyana cewa duk wani yunƙurin juya kalaman Shettima a matsayin suka ga gwamnatin yanzu ko wata alama ta rikici tsakanin manyan jami’an gwamnati, labari ne na ƙarya da kokarin kawo rashin zaman lafiya, don haka Shettima da Tinubu suna aiki tare domin kare dimukraɗiyya da doka a Nijeriya.

By Babaji