
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta kirayi al’ummar jihar da su halarci taron gudanar da sallar roƙon ruwa da aka shirya, wanda za a yi a ranar Asabar.
Za a yi sallar ne da nufin neman agajin ubangiji bisa rashin wadataccen ruwan sama a jihar kasancewar damina ta yi nisa.
Shugaban Majalisar, Shaikh Ibrahim Khalil ya sanar da hakan a wata takarda, inda ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon ƙarancin ruwan sama a wannan shekarar duk da ce yanayin damina ya yi nisa.
Da misalin ƙarfe 9:00 na safe ne za a gudanar da sallar a Masallacin Umar Bin Khaɗɗab dake hanyar zuwa Zariya.
Kazalika, Majalisar ta yi kira ga al’umma da su bada haɗin kai wajen neman rahamar Allah game da al’amarin.

