‘Yan bindiga sun kashe mutane shida a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan bindiga a Katsina sun shiga ƙauyen Jargaba ƙaramar hukumar’ Bakori inda suka kashe mutane shida da raunata yara biyu.

Ɗan majalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Bakori Hon Abdulrahaman Ahmed ya sanarwar manema labarai.

Ya bayyana cewa ‘yan bindaga ɗauke da mayan makamai suka shiga ƙauyen Jargaba inda suka wuce zuwa wata majalisar wasu mutanen ƙauyen inda suke hira”nan take suka bindige mutane shida har lahira.

Cikin waɗanda suka kashe harda mataimakin shugaban jami’in tsaro na CWC a ƙaramar hukumar Bakori,”Ɗan majalisar ya ce.

“Ɗan majalisar ya ƙara da cewa sun kuma ji ma wasu yara rauni, sannan sun shiga wani gida duk dai a ƙauyen Jargaba inda suka tafi da mata biyu.

Daga nan sai ɗan majalisar dokokin ya yi wa iyalan waɗanda aka kashe addu’ar Allah jiƙan su da rahama yaba iyalan juriya haƙurin rashi da suka yi.

Ƙaramar hukumar Bakori da ke kudancin Jihar Katsina na ɗaya daga cikin Ƙananan hukumomin da ƴan bindiga suka ɗaiɗaita.

By ukarofi