Kotu ta yi watsi da ƙarar da Abba Hikima ya shigar a madadin mabaratan Abuja

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Bar Abba Hikima ya shigar akan marasa galihu shigar, ciki har da masu bara, ‘yan talla da masu jari bola, inda ya buƙaci a biya su naira miliyan 500 saboda keta musu haƙƙin ɗan Adam da suka ce Ministan Abuja, Nyesom Wike, da Sufeto Janar na ‘yan sanda suka aikata. Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin ranar Juma’a, 11 ga Yuli, 2025, yana mai cewa ƙarar ba ta da tushe balle makama.

A cewar mai shari’a Omotosho, babu wata hujja mai inganci a cikin takardun da aka gabatar da zai nuna an take haƙƙin waɗannan mutane. Ya ce hujjar da lauya mai ƙara ya gabatar kawai rahotanni ne daga jaridu na yanar gizo da ba su da sahihanci domin ba a tabbatar da su daga ɗakin karatu na ƙasa kamar yadda Sashe na 156 na dokar shaida ta tanada.

Ya ƙara da cewa dogaro da rahotannin jaridu don tabbatar da gaskiya bai da amfani a gaban kotu, domin rahoton jarida na iya kasancewa an ƙirƙire shi ne don ya ba da tushe ga ƙararraki marasa amfani. Ya ce idan aka yarda da hakan, za a buɗe ƙofa ga ɗaukacin jama’a su riƙa garzayawa kotu da ƙarar da ba ta da tushe, wanda hakan zai dagula tsarin shari’a.

Tun farko dai, waɗannan marasa galihu sun buƙaci kotu ta tabbatar da cewa kama su ba bisa ƙa’ida ba, tsare su ba tare da tuhuma ba, da cin zarafi da karɓar kudi da ƙarfi, duk sun saɓa wa dokokin kare haƙƙin ɗan Adam. Sai dai kotu ta bayyana cewa wannan ƙara ba za ta kai ko’ina ba saboda rashin hujja mai ƙarfi, tare da watsi da buƙatarsu ta diyyar naira miliyan 500.

By ukarofi