Tinubu ba shi da ikon cire zaɓaɓɓen gwamna kamar yadda Shettima ya faɗa – Jam’iyyar ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC, ta yi tir da abinda ta kira da saɓa wa doka wajen tsoma baki a harkar siyasar Jihar Ribas, inda ta ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da iko a hukumance na cire zaɓaɓɓen gwamna.

A sanarwar da ke ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaranta, Mallam Bolaji Abdullahi, ADC ta goyi bayan kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima na cewa Shugaban ƙasar ba shi da ikon cire ko da zaɓaɓɓen kansila ne daga muƙaminsa balle a ce gwamna.

Duk da cewa Faɗar Shugaban Ƙasa ta yi ƙoƙarin fito da bayanin kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasar a fili duba da yadda ya haifar da cecekuce, ADC ta ce hakan yunƙuri ne na ƙoƙarin gyara kure a siyasa, wanda a madadin haka da mataimakin shugaban ƙasar ya tsaya akan matsayarsa, inda ta ce hakan shi ne haƙiƙanin tabbatar da gaskiya da bin tsarin dimukraɗiyya.

Jam’iyyar ta yi ikirarin cewa abinda ya sa aka nemi cire gwamna a zamanin Shugaba Goodluck Ebele Johnathan a Borno, shi ne ya sa aka cire na a Ribas a yanzu, lamarin da ta ce na farkon ya girmama dokar ƙasa saɓanin na yanzu.

Ta bayyana cewa, Shugaba Jonathan ya ƙaurace wa tsige Shettima ne da ke fama da matsin rashin tsaro a jiharsa bayan samun shawarar shari’a daga Kakakin Majalisar Wakilai na lokacin, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Antoni Janar na Ƙasa Mohammed Bello Adoke.

A ƙarshe, ADC ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta dawo da mulkin tsarin dimukraɗiyya a jihar Ribas ƙarƙashin jagorancin Siminalayi Fubara, da kuma bai wa al’umma haƙuri akan dakatarwar da ya masa.

By Babaji