Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata mata a Jihar Kano mai suna Hafsatu Yusuf, wacce ta haifi ‘yan biyar a Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano, ta rasu jim kaɗan bayan haihuwar da ta yi.
Jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Nabilusi Abubakar ƙofar Na’isa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja a ranar Alhamis.
Kofar Na’isa ya bayyana cewa, matar ta rasu ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare a asibitin, yayin da ta fuskanci zubar jini mai tsanani bayan haihuwar jariran.
A cewarsa, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na daƙile zubar jinin da kuma ceton rayuwarta, hakan bai yi nasara ba.
“Tun bayan haihuwar take fama da zubar jini, kuma duk ƙoƙarin da likitoci suka yi don shawo kan lamarin bai yi tasiri ba,” inji shi.
K/Na’isa ya ƙara da cewa an riga an yi jana’izar marigayiyar bisa koyarwar addinin Musulunci a gidanta da ke Hotoro.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su tallafa wa jariran da nono da sauran muhimman kayayyaki domin kula da su.
An haifi jariran guda biyar ne, maza uku da mata biyu, kuma an tabbatar cewa suna cikin ƙoshin lafiya, inda suke karɓar kulawa ta musamman a asibitin.
Rahotanni sun nuna cewa wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ta ɗauki nauyin kula da lafiyar uwa da jariranta bayan haihuwar da aka yi a asibitin.
A baya, ma’aikatar lafiya ta jihar ta bayyana cewa an yi nasarar haihuwar jariran, tare da sanya su da mahaifiyarsu a kulawa ta musamman.
Mijin marigayiyar, Malam Salisu Nufi’u, ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa tallafin da ta bayar, yana mai cewa taimakon ya zo a kan lokaci.
Gwamnatin jihar Kano ta kuma jaddada aniyarta na inganta harkokin kiwon lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, tare da rage mace-macen mata a lokacin haihuwa.
