Jirgin Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba da aiki yau – NRC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Gudanarwa ta Ma’aikatar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta bayar da sanarwar cewa jirgin da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna zai ci gaba da aiki yau Asabar kamar yadda aka saba.

Hukumar ta fitar tsari da kuma lokutan yadda jirgin zai ci gaba da gudanar da aikinsa, inda ta ce yanzu da ƙarfe 09:50am jirgin zai riƙa tashi daga Idu, Abuja, sai kuma ƙarfe 10:50am daga Rigasa, Kaduna.

Sanarwar hukumar ta nuna cewa, sauran jiragen ma za su ci gaba zirga-zigarsu babu tsaiko.

Daga nan, hukumar ta yi amfani da wannan dama wajen bai wa al’umma haƙuri kan duk wani akasi da aka samu sakamakon tangarɗar da jirgin Abuja zuwa Kaduna ya fuskanta a wannan mako mai ƙarewa.

A Larabar da ta gabata wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka kai hari tare da lalata wani sashe na layin dogo ta hanyar amfani da abu mai fashewa wanda hakan ya haifar da tsaiko ga tafiyar jirgin.

Bayanani sun tabbatar da cewa harin na Laraba ya auku ne tsakanin Dutse da kuma Rijana yanki da aka ce ya yi ƙaurin suna wajen harkokin ‘yan ta’adda.

Amma duk da aukuwar harin, Manajin Darakta na hukumar NRC, Fidet Okhiria, ya ce hukumar na bakin ƙoƙarinta wajen ganin jirgin ya ci gaba da zirga-zirgarsa a wannan hanyar.