Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Kungiyar Jama’atul Nasarul Islam ta samu tallafin takin zamani da taimakon gwamnatin Jihar Kano wanda Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Ahmad Bola Tunubu ta ke bai wa ƙungiyoyi domin bunƙasa noma a Nijeriya.
Tallafin, wanda ƙungiyar Jama’atul Nasarul Islam ta samu itama ƙungiyar Kiristoci ta KAN ta samu irinsa a takin zamanin kamar dai yadda Ibrahim Muhammad Wudilawa, Sakataran ƙungiyar Nasarul Islam na Jihar Kano ya bayyana a hirarsa da menama labarai a ranar Asabar da ta gabata bayan kammala taron da shugabannin ƙungiyar na ƙananan hukumomin 44 da aka yi a harabar ƙungiyar da ke Kano.
Har ila yau ya ce an tsara yadda rabon zai kasan ce a tsakanin ’yan ƙungiyar JNI da kuma yadda zasu aika da sunayansu, domin samun tallafin na gwamnatin tarayya da gwamati zata raba musu na su tabbatar da cewa wanda ba a taɓa bashi irin wannan tallafi a baya ba shi za a bai wa a yanzu kamar dai yadda sharaɗin samun takin yake a tsare.
A ƙarshe Wudilawa ya yabawa gwamnatin tarayya kan wannan talafin wannan takin zamani ga JNI inda kuma yanzu haka wannan ƙungiya ta na nan ta na cugaba da aiyukan ta na akaji da kuma ƙoƙari na cigaba da bada gudummawa ga maniyyata zuwa aikin haji tun daga Nijeriya har zuwa ƙasa mai tsarki da dawowar alhazai duk da canje-canjen da aka samu na rashani ba da tallafi ga Alhazan Nijeriya amma dai ƙungiyar amma dai ƙungiyar na nan ta yin ƙoƙarin ta na abun da za ta iya na tallafi ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajji kuma ba da daɗewa ba za su kai ziyara ta musamman ga shugaban hukumar alhazai ta Nijeriya NAHCON Farfesa Saleh Pakistan domin tabbatar da nasara a wannan harka ta taimakon maniyya ta.
Itama Amira Halima Muhammad Baƙo mai kula da harkar lafiya ta JNI, ta ce wannan tallafi suna gode wa duk kanin masu ruwa da tsaki a wannan tallafi na taki dan rabawa membobin su don bunƙasa noma a Nijeriya.