Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Kungiyar matasa masu rajin tabbatar da gaskiya, zaman lafiya da kuma tabbatar da ’yancin ɗan adam da ake kira ‘Upward Youth Accountability Peace And Human Right Intiatiɓe’ (YAPHI) ƙarƙashin shugabancin Kwamandan ta Tahir Idris Yakubu, ta samu yabo daga cibiyoyin da hukumomin tsaron Nijeriya, dangane da yadda ta ke aiki da kuma shirya taro da na horar da ƙungiyoyin tsaron sa-kai da ta yi a birnin Kano.
Taron ya samu halartar hukumomi da cibiyoyin tsaro a ƙasar nan wanda ya gudana a ranar Lahadi da ta gabata a birnin Kano.
Taron wanda ya samu halattar wakilcin rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano wanda kakakin rundunar ’yan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya wakilta, ya bayyana gamsuwar kan irin wannan ƙoƙari da ƙungiyar YAPHI ta gabatar a wannan lokaci inda kuma ya yaba matakan wannan ƙoƙari na yunƙurin taimakawa jami’an tsaro kan harkar wayar da kan al`umma yadda za su bawa hukumomin tsaro haɗin kai domin haɗa hannu na ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da tsaro a Kano da najeriya musammamma bita da aka shiryawa jami`an tsaron sa-kai na Kano.
Haka shi ma SC Muhammad Lawan Falala, babban kwamandan na hukumar NSCDC da ya samu wakilcin DSC Abubakar Kalgo, wanda kuma ya gabatar da takardar jawabinsa kan illolin lalata da satar kayan gwamnati, ya ce wannan ɗabi’a ce mara kyau mai illa wajen cigaban ƙasa kuma wannan taro da aka gayyaci wannan hukuma ƙarƙashin shugaban ta na Kano abu ne mai kyau na ƙarfafa gwiwar al’umma da ƙungoyi su cigaba da ba da haɗin kai ga jami`an tsaro domin cigaban zaman lafiya da kwanciyar hankali dama Nijeriya bakiɗaya.
Ya tabbatar cewa ƙungiyoyin sa kai na tsaro irin su, bijilanti da sauran su na da rawar takawa wajan wayar da kan al’umma na su cigaba da bawa jami’an tsaro haɗin kai a ko ina a kowana lokaci.
Shi ma ɗaya daga cikin manyan baƙi kuma ƙorarre a akan sha’anin harkar tsaro na duniya wanda ke gabatar da jawabai a kan dabarun tsaro a tarurrukan gida Nijeriya da sauran ƙasashan duniya mai kuma wayar da kan dabarun tsaron kare kai a kafofin yaɗa labarai a jaridu da rediyo talabijin da saurin su, Detectiɓe Auwal Bala Durumin iya jami`in tuntuɓa kuma shugaban cibiyar First ƙuality Assurance In Nigeria, ya bayyana cewa akwai buƙatar duk wani jami`in tsaro daga na hukuma zuwa na sa kai su tabbatar su na samun ilimi na ƙorewar tsaro na daidai da yadda laifuffuka ke canzawa kuma irin wannan taro abu ne mai kyau da ya kamata ƙungiyar YAPHI ta cigaba da shirya shi domin amfanin masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro domin bunƙasa shi.
Shima shugaban NPUPS, Kwamanda Ibrahim Adamu, ya bayyana jin daɗin sa kan wannan horon da aka yi a wannan rana, shi ma Isah Sulaiman Muhammad Shugaban Emergency Peace Security EPC, ya ce sun samu ƙarfin gwiwa a wannan taron bita.