Ka daina ba wa gwamnoni kuɗaɗen cire tallafin fetur – Jigon APC ga Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jigon jam’iyyar APC a Jihar Neja, Hon. Jonathan Vatsa ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya yi amfani da kuɗaɗen da gwamnati ta samu a sakamakon cire tallafin man fetur wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba a madadin ba wa gwamnoni.

Waɗannan kalamai na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohin Nijeriya da su daina amfani da kuɗaɗen al’umma wajen gina manyan gadoji.

Babban ɗan APCn, wanda shi ne sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na farko, ya bayyana haka ne a wata hira da ‘yan jarida a jiya Asabar a Minna, inda ya ce yana da kyau Tinubu ya yi amfani da salon marigayi tsohon Shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha na Asusun Kuɗaɗen Fetur (PTF) da tsarin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan na SURE-P.

Ya ce, ‘yan Nijeriya suna fuskantar matsi saboda wasu gwamnoni suna gudanar da ayyukan da ba su ake buƙata ba a madadin ƙaddamar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen inganta al’umma da harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

Da yake tsokaci kan kalaman shugaban ƙasar na cewa gwamnoni sun gina gadoji a wuraren da babu cinkoson ababen hawa da kuma nuna cewa hakan ayyukan ci-gaba ne da ake buƙata, jigon ya bayyana samar da gadojin a matsayin hanyar tsiyayar da kuɗaɗen al’umma daga ɓangaren gwamnonin.

Hon. Vatsa ya ƙara da cewa, bisa la’akari da kalaman Tinubu, “ya nuna cewa yana sane da gwamnonin nan sune babbar matsalar gwamnatinsa da jam’iyyar, yana mai kira a gare shi da ya dakatar da ba su kuɗaɗe sama da kima saboda al’umma ba sa amfana daga hakan.

Kazalika, ya kuma alaƙanta ƙoƙarin dawowa daga rakiyar gwamnatin APC da al’umma ke yi da matsin da ake fuskanta a ƙasar wanda a cewarsa, wasu gwamnoni sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsintar ƙasar a halin da ta samun kanta aciki.

By Babaji

Leave a Reply