
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar Sojojin sama ta fara gudanar da bincike game da lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’inta da wasu fararen hula a Unguwar Gangare dake Barakallahu a Jihar Kaduna.
Lamarin ya kuma sabbaba jikkata wasu da dama.
Daraktan yaɗa labaranta, AVM Olusola Akinboyewa ya tabbatar da al’amarin, inda ya ce ana bai wa waɗanda suka samu raunuka kula a Asibitin 461 NAF na rundunar.
Rundunar ta koka game da rashin da aka yi tare da jajenta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yayin iftila’in.
Ya kuma tabbatar masu da cewa za a gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike tare da yin adalci.
Haka kuma ya yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula a yayin da rundunarsu ke ƙoƙarin tabbatar da adalci a lamarin.
