Rundunar ƴan sanda ta fara gwajin lafiya ga kuratan da aka ɗauka a 2022

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta fara gudanar da gwajin ƙwaƙwalwa ga masu neman aikin kurtun ɗan sanda na shekarar 2022 a cigaba da aikin tantancewa.

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne aka fara aikin wanda kuma za a kammala a ranar 12 ga watan Maris a rukuni 17 na rundunar dake faɗin Nijeriya.

Jami’in yaɗa labaran rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata takarda, inda kuma ya yi kira ga masu neman aikin da su duba shafukan yanar gizo ta adireshin da suka nemi aikin don ganin matakin da suke tare da cire kwafin takardar gayyatar da aka yi musu.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za a gudanar da tantancewar bisa gaskiya da adalci a yayin zuwa zango na gaba na aikin.

Kazalika, ya yi kira ga masu neman aikin da su kiyaye sharuɗɗan da aka gindaya masu.

By Babaji