Kalubalen jingine koyarwa a harshen gado a ƙananan makarantun Nijeriya 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar dangane da batun jingine tsarin koyar da yaran makarantun firamare da ƙananan makarantun sakandire, cikin harshen uwa, wanda a baya yake ƙarƙashin Tsarin Ilimi na ƙasa, ta zo wa ’yan Nijeriya da dama a bazata. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ne ya sanar da wannan babban saƙo da kansa a yayin da yake jawabi a wajen taron Majalisar Kula da Harkokin Koyarwa ta ƙasa wanda aka gudanar a birnin Akure na Jihar Ondo. Ministan ya yi bayyanin cewa za a koma amfani da harshen Turanci a matsayin harshen koyarwa daga matakin farko har zuwa jami’a baki ɗaya.

Shi dai wannan tsarin da aka rushe, shi ne wanda aka kafa a shekarar 2022, wanda ya buƙaci a fara koyar da yara daga matakin farko ta amfani da harshen gida ko na muhalli domin inganta fahimtar yara da kuma tallafa wa harsunan gida. Amma Ministan Ilimi ya ce bayan nazari da bayanai da aka tattara daga makarantu daban-daban a jihohin ƙasar nan, an gano cewa yaran da aka fi koyarwa cikin harshen gida sun fi fuskantar matsaloli wajen jarabawar kammala babbar sakandire, kamar WAEC, NECO, da JAMB, musamman ma wajen fahimtar harshen Turanci da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban su na gaba.

Dr. Alausa ya ƙara da cewa, wannan mataki na mayar da harshen Turanci a matsayin harshen koyarwa an ɗauke shi ne bayan samun hujjoji masu yawa da aka tattara, ba wai akan zato ko ganin dama ba. Sai dai ya buƙaci duk wani wanda ke da wata fahimta ko ra’ayi na daban da ya saɓa wa wannan to, yana iya gabatar da bayanansa masu gamsarwa don tattaunawa bisa hujja.

A cewar Ministan, koyarwa ta harshen gida ta yi tasiri mara kyau wajen cimma nasarar yara a fannin karatu, inda ya nuna cewa tsarin gidan yana kawo matsala sosai a yankuna daban-daban na Nijeriya saboda bambancin harsuna a yankuna daban-daban. Wannan ya sanya gwamnati ta yanke shawarar mayar da Turanci a matsayin harshen koyarwa da kuma aikin gwamnati gaba ɗaya, domin samar da daidaito. 

Wannan shi ya kawo ƙarshen cece-kucen da ake samu a tsakanin malamai da ke ganin wannan tsarin takurawa ce a gare su, saboda ko dai suna ganin sun koyi ilimin koyarwa a harshen Turanci ne, ko kuma su ma kansu ba su ƙware wajen rubutu da karantu a harshen su na gado ko na al’ummar da suke ciki ba. A wani bincike da na gudanar game da tasirin tsarin koyarwa cikin harsunan gida, na gano cewa abu ne mai kamar wuya, a samu damar aiki da tsarin a wasu jihohi, saboda ƙarancin ƙwararrun malamai, da kuma samun waɗanda za su iya koyarwa a cikin harshen. Sannan wasu malaman su kansu ba sa jin harshensu na gado yadda ya kamata, ballantana su koyar da shi.

Wannan sanarwa harwayau, ta ɗauki hankalin malamai, iyaye, da jama’a daban-daban dake ta muhawara akai da faɗin albarkacin bakinsu. A ɓangaren malamai wasu na bayyana cewa, mayar da tsarin koyarwa zuwa harshen Turanci zai iya taimaka wa yara wajen samun sakamako mai kyau, musamman idan aka duba sakamakon jarabawar ƙasa da aka samu a shekarun baya. Suka ce koyar da harshen gida ba tare da ingantaccen tsarin koyarwa da dabaru ba, yana rikita ƙwaƙwalwar yara da jefa tunaninsu cikin rashin fahimta, musamman wajen koyon Turanci.

Wasu kuma suna nuna damuwa ne kan cewa cire amfani da harshen gado zai rage kima da kuma darajar waɗannan harsuna, tare da yiwuwar hana yara jin sauƙin koyo a matakin farko na ilimi. Haka kuma, wasu na ganin cewa wannan mataki na iya kawo tsaiko wajen raya harsunan gado da raya al’adun gargajiya na ƙabilu daban-daban a Nijeriya.

Lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta fitar da sanarwa kan ƙarfafa tsarin koyarwa cikin harshen uwa kafin fitar sabuwar sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi, wani mai sharhi a kafafen sadarwa daga yankin tsakiyar Nijeriya, ya yi shaguɓe kan cewa, irin wannan tsarin ne yake mayar da Arewa baya, saboda a cewarsa koyon Turanci da iya mu’amala da shi a harkokin kasuwanci da zamantakewa zai basu wuya sosai, da samar da komabaya a wayewar su da sanin rayuwa.

Kodayake, ita ma Ma’aikatar Ilimi a hujjojin da ta bayar, ta yi nuni da cewa harshen Turanci zai ba yara damar samun shiga matakai mafi girma na karatu a kowanne mataki na ilimi da rayuwa. Wannan yana da mahimmanci ƙwarai a wannan zamani na cigaban harkokin kasuwanci da ilimi a duniya baki ɗaya. Harsunan gado, duk da haka, za su ci gaba da kasancewa cikin tsare-tsaren ilimi ta hanyoyin da suka dace, amma ba a matsayin harshen koyarwa ba.

A hangen da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi dangane da wannan canjin tsari, tana ganin sauyin zai yi tasiri sosai ga yaran da ke rayuwa a karkara, saboda zai taimake su wajen inganta ilimin su na Turanci, kamar sauran yara a Nijeriya. Wannan sauyi harwayau, zai yi matuƙar tasiri ga yaran da ba su saba da harshen Turanci ba tun farko, sakamakon kasancewa harshen gado shi ne harshen da yara ke amfani da shi a gida kullum.

Sai dai kuma masana harkar koyarwa sun yi hasashen wannan sabon tsari zai ƙara samar da komabaya a tsarin koyarwa a karkara, saboda tun farko da yawan yaran ba sa samun sauƙin fahimtar Turanci a matakin farko na karatun su. Tsohon tsarin koyarwa da harshen gida na bai wa yara damar fahimtar ilimi cikin sauƙi da nutsuwa, yana kara musu ƙwarin gwiwa da natsuwa wajen koyon sababbin abubuwa. Don haka ake ganin cewa cire wannan tsarin zai sanya yaran karkara cikin matsalar fahimta, musamman ma idan ba a samu ingantaccen horo da kayan aikin koyarwa da za su taimaka wajen koyar da harshen Turanci ba.

Masu sukar wannan canji suna nuna damuwa cewa rashin koyarwa cikin harshen gida zai sanya yaran karkara da sauran yara su rasa alaƙa da al’adunsu da harshensu na asali. Zai kuma ragewa harshen gida kima, kuma zai haifar da komabaya a tsakanin matasa wajen kishin al’adun su na gargajiya da tarihinsu.

Bugu da ƙari, masu wannan ra’ayi na cewa wannan mataki na iya ƙara rura wutar rashin daidaito tsakanin yaran dake rayuwa a birane da na karkara, saboda yaran karkara ba su da damar samun kayan koyo da horo mai kyau a harshen Turanci kamar yadda yaran birni suke da shi.

Rushewar wannan tsarin koyarwa a cikin harsunan gida da maida hankali kan harshen Turanci zai haifar da canji mai girma a tsarin ilimi a ƙasar nan. Kamar yadda wannan mataki ya kawo muhawara mai zafi a tsakanin malamai da al’umma, wanda kuma zai buƙaci cikakken bincike da tattaunawa bisa bayanai na kimiyya da ƙididdiga kafin a samu matsaya ta ƙarshe mai ɗorewa.

Lallai akwai buƙatar samar da tsare-tsaren horo na musamman wanda zai taimaka wa malamai wajen inganta dabarun koyarwar su, tare da samar da kayayyakin koyarwa na zamani da kayan karatu da za su taimaka a aji. Wannan zai haɗa har da buƙatar samar da haɗin gwiwa da ƙungiyoyi dake ba da tallafi kan harkokin ilimi irinsu British Council, don samun tallafin horar da malamai, bunƙasa ƙwarewa kan harshen Turanci da jagorancin makarantu. 

Sannan akwai buƙatar haɗa kai tsakanin hukumomi daban-daban, masana harshe, da gwamnatoci na jihohi domin tabbatar da cewa malamai sun samu isasshen horo da kayan aikin da za su inganta koyarwa da fahimtar sabon tsarin. Haka zalika, an yi amfani da sababbin hanyoyi na zamani kamar fasahar dijital da manhajoji na koyarwa don tallafa wa malamai wajen inganta karatun yara.

By ukarofi

Leave a Reply