Kamar gwamnati ke ƙara ta’azzara matsalolin Nijeriya

Spread the love

A ɓangare guda za mu iya cewa haƙiƙanin gaskiya Gwamnatin ƙasar mu ta Nijeriya suna ƙoƙari, suna kuma aiki don ganin an tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki. Amman duk da wannan ƙoƙarin har ila yau ita ce babbar matsalar ƙasar.

Ta kowane ɓangare na matsalar ƙasar nan, za ku ga akwai gazawar ita gwamnatin. Musamman ɓangarorin tsaro, da kuma ita kanta matsalar tattalin arzikin ƙasar da kuma fannin ilimi.

Bari mu fara da harkar tattalin arziki a wannan karon. Idan muka yi duba I zuwa harkar, zamu ga cewa, kuɗin da ƙasashen waje suke samu daga Nijeriya, ya fi kuɗin da Nijeriya ke samuwa da ga gare su. Mu duba harkar mai, Ɗangen mai Nijeriya ke fitarwa, sannan sai bayan an tatse sai a kawo mana tatsatsen mu saya. Wanna fanni kamar misalin manomi ne ya noma Gyaɗa, sannan ya saida gyaɗan ga ɗan kasuwa, shi kuma ɗan kasuwa ya sarrafa ta, ya cire kuli-kuli a ciki, ya kuma cire mai. Lokacin da manomin ya sayar da gyaɗana, ya sayar da ita ne a farashin Naira 500, shi kuma mai sarrafa ta ya sarrafa mai aƙalla na Naira 400, ga kuma ribar kulili shima zai kai Naira 300, ka ga kuma tunkusa a gefe na yin fiyan agusi ko ko alaiho. Sannan manomin yana sayan mai na miya naira 100 ko wanne rana, don Allah ina ribar ta ke a nan?

To haka misalin Nijeriya, muna sayar da ɗanyen mai ga ƙasashen waje, sannan mu sayo fetur da Gas daga gare su. Bayan kuma sun gama tatsan abubuwa masu muhimmanci, wanda za su sarrafa wani abu na fasaha sannan su kawo mana mu saya.

Har iya yau, a fanni tattalin arzikin, mu ke zuwa ƙasashen waje mu sayo kayayyakinsu, a maimakon gwamnati ta yi ƙoƙarin samar da abubuwan nan a ƙasar sai kawai tarungumin tafiya waje ɗan sayo kaya. Sannan mu ke zuwa ƙasashen wajen hutawa, gwamnati batayi mana kayayyakin hutawa a ƙasar ba. Duk saboda wani ya fita ƙasar wajen, to gwamnatin ƙasar tana samun wani abu, amman mu kuma Nijeriya samun mu na raguwa.

Misali, ba bu asibitocin zamani a ƙasar, duk wata cewa babba, sai an tafi waje, za a kashe kuɗin jirgi, kuɗin aiki, kuɗin zama a ƙasar, domin duk kasa da za ka ce dole sai Gwamnatin ga tabbatar da za ta samu ribar daga gare ka in ba haka ba, ba zasu barka kayi koda kwana ɗaya ba a ƙasarsu. Su ba irin Nijeriya bane, da ko wane mutum zai iya shigowa ba tare da bincikarsa takardun shaida ba. Ba a tambayar ɗan wata ƙasa idan zai shigo Nijeriya me ya zo yi. Kuɗi kawai nayin aikin, da zarar an baiwa mai gudanar da binciken kuɗi shikenan buƙata ta biya kuma wannan shine rashawa da cin hanci. Kuma duk daga gwamnatin Nijeriya ne.

Ziyarar ƙasar waje, shugabannin mu na son kai ziyara wata ƙasa, amman ba ko wane shugaba bane ke son kawo ziyara Nijeriya. Daga hawan Tinubu zuwa yanzu ya zagaye ƙasashe da yawa, gaya min shugabanin ƙasashe nawa ne suka zo Nijeriya? Duk fitar da Tinibu kuɗaɗe nawa ake kashewa, sannan kuma ribar nawa yake samu? Gwamnonin mu ke anfani da kuɗin jiha su je ƙasar waje, wa ga taɓa jin wani gwamna daga wata ƙasa ya kawo ziyara Nijeriya? To mu nan ba Gwamnan ba, har Sanata babu wanda bai taɓa zuwa ƙasar waje ba, kuma da kuɗin mu suke anfani. Taya ƙasa tattalin ba zai lalace ba?

Mu dawo harkar Ilimi, kamar yadda na fara bayani, ba a damu da harkar ilimi a Nijeriya ba. A Nijeriya ne zaka samu wanda yayi karatu amman ba aiki karatun shi ya zama a banza. A Nijeriya ne za ka samu mutum da digiri ɗin shi amman tsabar damuwa ta sa ya manta komai. Ana anfani da kuɗin makaranta ana zuwa wata kasar dan gina su, yayin da kuma namu makarantun na rugujewa.

Mu dawo fannin yaƙi da rashawa, wallahi, tallahi, ba za a taɓa daina rashawa a Nijeriya ba har sai gwamnati ta zama bata da rashawa. Domin a wannan fannin, za ka samu mutum yana cin hanci, amman kuma yana yaƙi da cin hanci. Jami’ai nawa, suke yaƙi da cin hanci da rashawa, amman sune manya a wajen chin hanchi? Su kan su ma, basu zo wannan matsayin ba sai da suka bada cin hancin.

Maganar tsaro, wannan ta ma fi muni, za ka ga sojoji da ’yan ta’adda, duka suna kashe mutane. Dukan su makasa ne, harkar tsaro ya munana, zamu haɗu a mako na gaba ɗan warware wannan mas’ala tsaf, zaku fahimci cewa gwamnatin ita kanta ma ’yar ta’adda ce, da hannun ta ake wannan ɓarna, idan kuma ba haka ba, me yasa har yau an kasa kawo ƙarshen matsalar tsaro? Zan yi cikakken bayani, Insha Allah.

Daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].

 
By ukarofi