Kamfanin siminti na BUA ya tallafa wa lauyukan dake maƙwabtaka da shi

Daga AMINU AMANAWA minu a Sakkwato

A wani mataki na tallafawa ƙauyukan dake maƙotaka da shi, kamfanin sarrafa siminti na BUA ya samar da asibiti, makaranta, rijiyar burtsatse dama masallaci ga lauyukan Gidan Boka da Gidan Marafa dake a Ƙaramar Hukumar Mulkin Wamakko.

Da yake hannun ta kayan ka al’ummomin ƙauyukan shugaban kamfanin, Yusuf Binji ya bayyana cewa wannan ƙoƙari da kamfanin ya yi na daga cikin irin gudunmawar da yake bayarwa ga al’ummomin dake maƙotaka da shi.

Binji wanda shugaban sashen hulɗa da jama’a na kamfanin Sada Suleiman ya wakilta, ya bayyana cewa baya ga wannan sama da ƙauyuka 68 dake maƙwabtaka da shi, sun amfana da tallafin siminti ton 170 domin gudanar da ayyukan gina gidajensu.

Ƙauyukan kuwa sun haɗar da Gidan Bailo, Gantsare, Gidan Datti, Gidan Mai tuta, Gidan Boka, da Gidan Gamba da dai sauransu.

“Alhamdulillah ƙauyukan Gidan Boka da Gidan Marafa ƙauyuka ne da ayukkan kamfanin mu ya shafa mun tada su a baya da kuma samar masu da sabon muhalli, ta hanyar ba su filaye da diyyar wurarensu, kuma mun kashe sama da Naira miliyan 270 wajen samar masu da ruwa, wuta, hanyoyi, assibiti, makaranta, masallaci da sauran su.”

Da aka tambaye shi kan yanayin hulɗa da mu’amala da ƙauyukkan shugaban kamfanin ya bayyana cewa, suna da kyakkyawar hulɗa a tsakaninsu da al’umma.

Shi ma da yake magantawa shugaban qaramar hukumar mulkin Wamakko Bello Haliru Guiwa, wanda mataimakinsa ya wakilta, ya gode wa kamfanin bisa ƙoƙarin da yake a koda yaushe wajen daɗaɗa wa ƙauyukan da yake makotaka da su.

Shi ma Ardon Wajaki Muhammad Mailato Gumbi godiya ya yi a madadin al’ummar da suka amfana tare da shan alwashin kula da su tamkar ƙwai.