Gwamna Tambuwal ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da aikewa da sababbin kwamishinan da ya naɗa a ma’aikatun su tare da yin garambawul ga wasu dake kai.

Sababbin mambobin majalisar zartaswa ta jiha da gwamna ɗin ya tura a ma’aikatun su sun haɗar da Dahiru Yusuf Yabo, da aka tura ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta jiha, Akibu Dalhatu yaɗa labarai da wayar da kan al’umma, da kuma zai kula da ma’aikatar matasa da wasanni kari da ta farkon, Bashir Muhammad Lambara, albarkatun ƙasa, yayin da Abdullahi Abubakar Dange, aka aike da shi a ma’aikatar kula da jin daɗi da warwala sai kuma Abdullahi Yusuf Hausawa da zai kasance jagora a ma’aikatar kula da harkokin cikin gida.

Waɗanda aka yi wa garambawul na ma’aikatunsu sun haɗa da Salihu Maidaji, ma’aikatar ayyuka, Bashir Gidado, ciniki da masana’antu yayin da ma’aikatar filaye da gidaje ta faɗa hannun Aminu Bala Bodinga.

Sauran sun haɗa da Abdullahi Maigwandu, ƙananan hukumomi da cigaban al’umma, Usman Suleiman Dan Madamin Isa, ma’aikatar kula da lamurran addini, sai Isa Bajini Galadanchi, da zai kula da ta raya karkara.

Ragowar sune Abubakar Maikudi Ahmad, tsaro da ɗaukar ma’aikata, Farfesa Aisha Madawaki, ilimi mai zurfi,  Hassan Muhammad Maccido, kasafin kuɗi da kula da tattalin arziki, Dokta Ali Inname, lafiya da kuma ma’aikatar kuɗi da zai kula da ita, yayin da jagorancin ma’aikatar makamashi da albarkatun man fetur dama kula da ta muhalli ya faɗa a hannun Aliyu Balarabe Dandin Mahe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *