2023: Zan bada kaso 40 na muƙamai ga matasa da mata – Atiku

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bai wa matasan Nijeriya tabbacin barin kyakkyawan tarihi gare su, idan aka ba shi damar jagorantar al’amuran ƙasar.

Atiku Abubakar ya bada wannan tabbaci ne lokacin da ya karvi baƙuncin tawagar shugannin PDP sabon ƙarni ƙarƙashin jagorancin babban daraktan ta Audu Mahmud a gidansa dake Abuja.

Ɗan takarar shugabancin ƙasar ya sake jaddada aniyarsa kamar yadda ta ke ƙunshe cikin kundin manufofinsa, na bai wa matasa dama a gwamnatinsa ta hanyar ware musu kaso 40, inda kuma ya ce zai yi sauye-sauyen da suka kamata domin bada dama ga mata da matasa.

Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa a gwamnatin PDP ne kawai aka aiwatar da tsarin nan na keɓewa mata kaso 35, inda ya ce APC ba ta tava girmama wannan yarjejeniya ba.

Ya kuma koka game da halin da matasa suka samu kansu, inda ya yi alƙawarin daidaita al’amuran. A saboda haka, ya ce ilimi zai zamo babban ginshiƙin gwamnatinsa domin bunƙasa rayuwar matasa da haɓaka dimukuraɗiyya. 

Ya bayyana takaici kan yadda APC ta wargaza tsarin da gwamnatin PDP ta shimfiɗa a baya.

A bayanin da mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yaɗa labarai ya fitar, ya bayyana cewa yayin da yake tabbatar da muhimmancin matasa wajen gina ƙasa, ɗan takarar na PDP ya jaddada cewar zai yi aiki da buƙatun zamani, tare da gudanar da gwamnati mai tafiya tare da kowa mai la’akari da bambance-bambancen dake tsakaninmu.

A nasa jawabin, jagoran ayarin, Audu Mahmud ya ce Atiku Abubakar wata maɓuɓɓuga ce ta ƙarfafa gwiwa da kyakkyawan tunani ga matasan ƙasar nan, inda ya bayyana yaƙinin da yake da shi na ƙwarewar Atiku domin magance matsalolin tattalin arziki da matsalolin siyasa domin amfanin dukkan ‘yan Nijeriya.