Kanku Musa: Mutum mafi arziki a tarihin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sarkin daular Mali, Kanku Musa ya kasance mutum mafi ƙarfin arziki da aka tava samu a duniya. Wadatarsa ta ba shi damar mayar da Timbuktu cikin birni mai ban mamaki. Ya yi sarauta tsakanin shekarar 1313 zuwa 1337.

An haifi Kanku Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Koda yake ana yawan kiran shi Kankan Musa, amma ainihin sunansa ‘Kanku’. Wannan sunan mata ne da ya samo asali daga dangin mahaifiyarsa. Wasu daga cikin manyan ƙabilun wancan lokacin sun fi danganta yaro da ɓangaren uwa, don haka maza ma suke ɗaukar sunan mahaifiyarsu.

A cikin shekarar 1313, bayan rasuwar wansa Sarki Abu Bakr II, Musa ya zama shugaban Daular Mali. A lokacin mulkinsa na tsawon shekaru da dama, ya yaɗa al’adun Musulunci a kewayen ƙasar Mali, kuma daular ta zama ɗaya daga cikin waɗanda suka cigaba a duniya.

Kanku Musa ya fito ne daga gidan sarauta na su Keita waɗanda suka yi mulkin Mali tsawon ƙarnoni da yawa. Ya kasance sarki mai wadata wanda ya gina daula mai qarfin faɗa a ji, kuma wacce ta bunƙasa. Bisa ga bayanan al’adar baka, kakansa Abu Bakr na farko, qani ne ga Sunjata Keita wanda ya kafa Daular Mali. Sarautar Musa ta haska daular Mali a duniya.

A shekarar 1324, Kanku Musa ya tafi aikin hajji a Makka. Ayarinsa ya ƙunshi mutum dubu 60 da bayi dubu 12 da dogarai da ke sanye da kayan kawa da sanduna na zinare waɗanda kuma ke kula da dawakai da kayansu.

Wannan ƙasaitaccen rangadin ya sa ya zama sananne, musamman a Yammacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin kowane gari da ya ya da zango, Musa ya kasance mai karamci sosai kuma ya yi ta ba da kyautar wani ɓangare na dukiyarsa – wanda babu shakka ya yi tasiri ga tattalin arzikin yankin, da kuma labarin mulkinsa.

Sarki Mansa Musa (Musa Keita) ya hau kan ragamar mulki a shekarar 1312 milladiya, bayan rasuwar Sarki Abu Bakr na biyu. Hawansa karagar mulki ke da wuya ya faɗaɗa iyakar masarautarsa wacce ta faro tun daga gaɓar ruwan Gambiya, har yankin ƙasar Sudan, inda ya haɗa yankin ƙasar Hausa da ke Nijeriya da ƙasar Nijar da Senegal, Burkina Faso, Gambia, Mali, Chad da Mauretania su suka haɗu suka bayar da Daular da Mansa Musa ke mulka. Babban birnita shi ne birnin Tumbukhtu wanda ya ke ƙasar Mali a yanzu.

Sarki Mansa Musa ya shimfiɗa mulki na qasaita, ya kuma faɗaɗa birnin Tumbuktu ta yadda y ayi gogayya da sauran manyan biranen duniya na wancan zamani.

A shekarar 1324 Sarki Mansa Musa ya shirya tafiya zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke Farali, tafiyar da ta barwa duniya tarihi na ban mamaki.

Lokacin da tawagar Sarki Mansa Musa ta motsa daga birnin Tumbuktu zuwa garin Makka, ya tafi da sojoji sama da dubu ashirin, haka zalika bayin da za su yi hidima sun haura ɗari biyar. Ya kuma ɗebi dukiya da zummar yin hadaya a garuruwa masu tsarki na Makka da Madina, dukiyar da ko sarakunan Daulolin Larabawa ba su tava mallakar irinta ba. Kamar yadda malaman tarihi suka ambato, sun ce  ya tafi da raƙuma dubu ashirin da dawakai dubu shida, da manya-manyan mazubai cike da zinare da azurfa, da tufafi na alfarma da sauran nau’ukan dukiya duk domin bayar da kyauta ga mutanen Makka da Madina.

A lokacin wannan tafiya tasa, ya tafi da wata amaryarsa wacce ya ke matuƙar ƙauna, wacce aka tanadar mata bayi da kuyangi sama da ɗai waɗanda aikinsu kawai yi ma ta hidima.

A yayin da tawagarsa ta ratsa hamadar arewacin Afirka, bayan tafiiyar watanni, sai wannan amaryar tasa ta gaji da tafiya a cikin Sahara, ta yi fatan ina ma ta samu dausayin mai danshi da za ta huta. Wannan buqata da ta nuna ya sa Sarki Mansa Musa ya umarci da a share Saharar a ƙirƙirar ma ta dausayi (Lambu) da za ta huta. A tarihin duniya wannan shi ne lokaci na farko da aka taɓa samar da dausayi a cikin Sahara.

An ce an yanka sama da rakuma dubu uku aka yi amfani da ruwan cikinsu aka samar da wani Dausayi mai tarin ni’ima da shuke-shuke masu ban sha’awa. A wannan Dausayin ne amaryar tasa ta samu damar hutawa har na wasu watanni kafin daga bisani tawagar ta sake motsawa.

Labarin wannan tawaga ta ratsa ko ina a ƙasashen Yankin Magrib. Sarakuna da dama sun kaɗu sun kuma firgita da ƙarfi da kuma tarin dukiyar da suka gani ta Sarki Mansa Musa.

Lokacin da tawagar ta isa ƙasar Misira, ya kiɗima Misirawa, domin basu tava ganin mutum mai ƙarfin dukiya kamar Mansa Musa ba. Ta yadda har ya kusan mayar da Misirawa bayinsa saboda tarin dukiyar da suka gani.

Labarin isowarsa Misira da irin dukiyar da ya ke ɗauke da ita ya watsu a kowane lungu da saƙo, wannan dalili ya sa mutane su ka yi ta turereniyar zuwa ganin wannan tawaga.

Malaman tarihi suka ce, Mansa Musa ya yi ta raba Hadaya (Kyauta) ga mabuƙata da Miskinai, har ila yau ya hidimtawa Malaman Misira na zamanin, ya bada dukiya mai yawa wajen sake gina Masallatai da makarantu. Saboda kyautuka da ayyukan alheri da ya yi ya sa aka samu hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar Misira.

Tawagar Mansa Musa ta tashi daga Misira ta nufi Hijaz (Makka) ta gavar ruwan Maliya. Tuni labarinsa da irin hidimar da ya yi wa Mutanen Misira ta isa garesu. Wannan dalili ya sa ya samu kyakkyawar tarba daga mutanen Makka da Madina.

Wannan tarin dukiya da ya taho da ita, sai ya tattara ta gaba ɗaya ya bayar da ita Hadaya ga Haramin Makka da na Madina, haka nan ya bi manyan gidajen Sharifai da na Zuriyar Sahabbai ya yi musu hidima ta ban mamaki. An ce Allah ne kaɗai ya san iya adadin zinaren da ya raba.

Sakamakon ɗimbin arzikin da ya mallaka, Kanku Musa ya gina wuraren addini da na mulki da yawa daga tun shekarar 1325. Daga cikinsu akwai masallatai, da makaranta da kuma masarauta a garuruwan Timbuktu da Gao.

Masallacin Sankore da ke Timbuktu ya kasance fasaharsa da ta fi fice. Ya ba da damar musayar al’adu tsakanin ƙasar Mali da ƙasashen Larabawa. Wasu ɗaliban Mali sun je Misra da Maroko don kammala karatunsu, yayin da wasu malaman Masar da Moroko suka je karatu a Sankore madrasa. A wancan lokacin ya kasance cibiyar yaɗa kyakkyawan al’adun Musulinci a Yammacin Afirka.