Ka na so iyalinka su riƙa girmama ka?

Daga AMINA YUSUF ALI

Me ya sa za ka nemi girmamawa wajen iyalanka? Saboda in dai har za ka samu wannan girmamawar daga matarka, lashakka za ka samu daga yaranka. Domin su yara suna kwaikwayon uwarsu ne. 

Ita wannan girmamawar a aure tana da matuƙar muhimmanci. Idan iyalinka ba sa girmama ka, ba za ka ji daɗin rayuwar auren yadda ya kamata ba. Haka idan ba girmamawa da mutuntawa da ƙimantawa, sam auren ma ba zai yi ƙarko ba. 

Menene girmamawa da mutuntawa?
Ba fa wai ta dinga jin tsoronka ba ne kawai shi ne girmamawar ba. A’a, ƙimanta umarninka a gaba da bayan idonka. Rashin ɗar da shakku a zuciyarta game da shugabancinka, shi ne girmamawa. 

Ta yaya za ka nema wa kanka girma a wajen iyalinka?

A ƙasar Hausa maza suna ƙoƙari matuƙa wajen ganin sun samar wa kansu girma da mutunci a wajen iyalansu. Sai dai da yawa ba sa bin hanyoyin da ya dace su bi:

A ƙoƙarinsu na neman girmamawar matansu, maza suna ƙoƙarin sanya tsoro a zukatan mata ta hanya duka, zagi, faɗa, cin mutunci, ƙarfa-ƙarfa, da sauransu. 

Rashin sakar mata fuska: maza suna ganin yawan sakar wa mace fuska shi yake jawowa ta raina ka. Rashin hira da ita, rashin sauraren damuwarta ko ra’ayinta ko shawara da ita. Haka rashin yaba mata idan ta yi maka kwalliya ko girki, da sauransu.

Haka nuna mata cikakken iko da tauye mata ‘yanci. Kamar hana ta zuwa unguwa idan ta tambaya. Ko kuma hana ta cigaba da karatu ko yin aikin albashi ko sana’a.  Shi a ganinsa idan ta samu sakewa za ta raina shi.

Ko kuma ta haɗu da waɗanda za su zuge ta, su sa ta raina shi. Amma anya ƙarfa-ƙarfa tana sa mace ta girmama ka? Ka yi tunani, Yayana. 

Nuna son a girmama shi ƙiri-ƙiri. A ƙa’idar rayuwa ma, duk masu son a girmama su ba su cancanci a ba su girman ba. Kuma girmamawa ba a nemanta ƙarfi da yaji. Kuma ko sun nema da wuya su samu. Gara ka bi a hankali da lallama ka samu. Ita mace a rayuwarta duk abinda ka tursasa ta, ta fi taurin kai da bijirewa. Idan kana ƙuntata mata, ita ma sai ta dinga neman hanyar ƙuntata maka yadda za ka ji yadda take ji. Ba dai girma kake so ba?

To ba za ta girmama ba. Abinda ka kasa fahimta, Yayana. Shi yaƙi ɗan zamba ne. Ita matarka fa a ɗabi’ance ma banda shari’a da ta yi umarni, kai ya kamata ma ta fi rainawa fiye da kowa a Duniya. Domin tana ganinka a yanayin da ba wanda yake ganinka. Wanne kuri kuma za ka yi mata? Wanne zare ido kuma za ka yi? Wanne dare ne jemage bai gani ba? Kawai dai a yi sha’ani. Gara ka yi dabarun cimma haka. 

Hanyoyin da za ka bi don samun girmamawar iyalinka?

Hanya ta farko ita ce, ka so ta kuma ka nuna mata son tsakani da Allah. Wasu za su ce soyayya kuma? Eh soyayya. Idan da so komai zai zo da sauƙi. Za ta girmama duk wata dokarka saboda ta san kana sonta ba ka yi dokar don ka cutar da ita ba. Idan akwai yarda kuwa, akwai girmamawa a ciki. 

Na biyu: ka tausaya mata. Tausaya wa mace yana sa girmanka ya qaru da qimarka a idanunta. Ta dinga ganin girmanka kamar na iyayenta. Domin a wajenta ɗabi’ar iyayenta ce su tausaya mata. Sai ga shi kai ma ka siffantu da wannan siffar. 

Ka girmama ta kai ma. Maza sun kasa gane cewa, da yawa daga ɗabi’ar da mace take yi a gidan aure su ne suke koya mata. Shi ya sa sai ka ga mace shiru-shiru amma daga an ɗauki wasu lokuta, sai ta birkice ta koma wata iri. Irin haka ne ai sai a rasa dalili. Kuma ko ba matarka ta aure ba, ko a wajen aikinka inda kake shugabanci ko a kan ƙanenka ne ma haka. Dole sai ka girmama mutum zai gane darajar girmanka ya girmamaka. 

Ka dinga girmama ra’ayinta da shawararta gare ka. Hakan zai sa kai ma ta dinga girmama naka. Kada ka dinga dinga dagewa a kan ra’ayinka dole shi ne ra’ayi. Kuma shawara ba lallai sai na gaba ke iya ganowa ya ba na qasa ba. Ko ɗanka zai iya ba ka shawara a kan abu, kuma ta yi maka amfani. Kuma hakan yana qara danƙon soyayya da fahimta a gidan auren wanda zai kai ga ƙara samun haɗin kai a tsakaninku. 

Na uku, ka tafiyar da rayuwarku bisa tsarin shari’a. Wannan ma zai ƙara maka ƙima a idonta. Don ta san kai ba azzalumin da za ta yi wa tawaye ba ne. Bin dokar Allah kake. Musamman idan kana da mace fiye da ɗaya. Kowacce ka yi mata adalci.

Kowacce ta yi maka ƙorafi, ka nuna cewa, kai fa ga hujjar yin haka a musulunci. Hakan zai sa ba matanka ko matarka kaɗai ba, ‘ya’yanka ma ganin girmanka za su yi. Abinda maza suke mantawa fa, su ‘ya’ya  kullum suna koyi da uwarsu ne. Haka suna son mai sonta da ƙin mai ƙuntata mata. Yi wa uwarsu adalci zai sa su ƙara ganin ƙimarka har ma su cigaba da tausaya maka ko da ka tsufa. Sannan akwai matan ma da gayya idan kana cutarsu za su dinga ba da ƙofa ‘ya’yanka su raina ka. An sha samun kesa-kesai inda ‘ya’ya suka kashe Ubansu ko suka dake shi a kan zaluntar uwarsu. Ban ce dai-dai ba ne hakan. Amma sai a kiyaye afkuwar hakan. 

Ka zama mai gaskiya a harshe da a aikace. An san ba kowa zai iya haka ɗari bisa ɗari ba, saboda ‘yanadamtaka. Amma ƙimarka za ta iya zubewa a idon iyalinka yayin da suka kama ka da ƙarya. 

Kar ka zama mai ƙuntata mata ta hanyar hana ta walwala ko fita ko mua’amala da wasu ko kallon fim da sauransu. An san kai ne da alhakin tarbiyyar iyalanka, amma kada ka zama ka matsa da yawa. Sai ka sa, ana bin umarninka a zahiri, amma a ɓoye, kai ne mutumin da ta fi tsana, ta fi rainawa a gidan Duniya. Haka idan kana mata tsawa ko duka ka guji sanda za ta goge ta iya ramawa ko shaiɗan ya zuga ta ta kashe ka ba fata ba. Ko kuma ‘ya’yanta suka kawo ƙarfi. Ko abin tsautsayi ka illata ta, ka gamu da hukuma. Da ma ba inda musulunci ya ce aure gidan kurkuku ne. 

Ka zama mai kyakkyawar mu’amala. Maza sun kasa gane kyawun mu’amalarsu yana saya musu girma da ƙima wajen matansu. Idan sun nemi abu ku yi musu. Idan aiki bai zama dole ba a sawwaƙe musu. Wallahi wannan ya fi duk wani muzurai da za ka yi mata tasiri. Kuma wannan mujarrabi ne, a gwada a gani. 

Kada ka zama mai girman kai. Kada ka nuna mata dole ita maƙasƙanciya ce a kanka. Ka zama mai sauqin kai, ka dinga yabawa, godiya gare ta, da ba ta haƙuri duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. 

Kada ka dinga nuna son kanka a kanta. Ko a wajen mu’amala ta aure. Ko kuma a wajen yin hidima. Kada ka dinga barinsu da yunwa ka je ka ci mai kyau a waje. Kada ka dinga barin su a tsumma kai ka dinga ɗinke-ɗinke kana fita. Hakan yana zubar da ƙimarka a idanunsu. 

Ka dinga riƙe amana a dukkan wata mu’amala da ta shiga tsakaninku musamman ta sirrinta ko kuɗi. Hakan zai sa ka zama abin girmamawa a idonta. Har ma a idon wani nata. Don za ta yi ta santi da ba da labari ga mutane. Domin riƙon amana yana daga cikin manyan kyawawan halayen da suke ɗaga darajar mutum a gurin kowa.

Haka girmama iyayenta yana sanya ta girmamaka kai da naka iyayen da ‘yanuwa. 

Ka zama mai mu’amala mai kyau da sauran mutane. Hakan za sa ta ɗauke ka mutumin kirki kuma ta dinga wimanta ka. 

Haka ta fuskar auratayya ka zama jarumin namiji. Akasin haka, zai kawo raini tsaninka da ita. 

Haka ka guji yin cacar baki da ita. Idan ta tunzuro, fice ka bar mata gidan. Za ta yi nadama. 

Haka kada ka bari ta kama ka da gulma ko tsaigumi. Maganganun da aka san mata da su dai. 

Sai na ƙarshe, wanda kuma shi ne ya fi kowacce dabarar da na lissafa a sama ƙarfi wajen sama maka qima gurin matarka shi ne, ɗaukar nauyinta a dukkan buƙatun rayuwa. Ina nufin abinda ya shafi harkar kuɗi. Kada ka bar ƙofa ko ta allura ce.

Ta ce ta cika kuɗin wani abu ko ta yi wa kanta ko yaranta kaza. Idan da hali ma, abinda ba nauyinka ba ma,  ƙara ka yi mata. Wallahi ina tabbatar maka, mace har sujjada sai ta kusan yi maka saboda girmamawa. Ku gwada wannan laƙanin nawa. Da ma idan kana so ka nemo wa kanka raini a sauƙaƙe, to ka yi wasarere da haƙƙin iyalinka ka ga ikon Allah.

Da fatan ‘yan uwanmu maza za su yi amfani da wannan dama domin su samar da zaman lafiya da yanayi mai kyau tare da walwala a cikin gidajenku.  Muna godiya ga masu kira da addu’a da ba da shawara da tsokaci. Ku sani ku kuke ƙara ƙarfafarmu a kullum. Na gode, mu haɗu a wani makon.

Ku cigaba da turo saƙonninku a akwatin Manhajariu mai farin jini!