Kano Pillars ta samu maki uku a kan Plateau United a gasar Firimiyar Nijeriya

Kano Pillars ta doke Plateau United 2-1 a gasar Firimiyar Nijeriya da suka kara ranar Lahadi a Jihar Katsina.

Kungiyoyin sun tashi ba ci a minti 45 ɗin farko daga nan suka je hutu, bayan da suka koma zagaye na biyu ne aka ci ƙwallayen uku.

Plateau United ce ta fara zura ƙwallo ta hannun Saka Gafar daga baya Pillars ta farke ta hannun Rabiu Ali, sannan Ahmed Musa ya ci na biyu daf da za a tashi.

Pillars za ta buga wasan gaba a gidan Bendel Insurance a babbar gasar tamaula ta Nijeriya.