Mahukuntan Gasar La Liga sun sanar da Robert Lewandowski a matakin gwarzon La Liga na watan Oktoba.
Karo na uku a jere da ’yan wan Barcelona ke lashe ƙyautar ta wata-wata da ake bayyana wanda ya fi taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.
Tun farko Raphinha ne ya fara karɓar ƙyautar, sai kuma Lamine Yamal daga nan Robert Lewandowski ya zama gwarzon La Liga na watan Oktoba.
Raphinha daga Brazil shi ne gwrazon watan Agusta, Yamal na Sifaniya ya zama na watan Satumba da kuma Lewandowski daga Poland na watan Oktoba.
Barcelona ba za ta manta da watan na Oktoba ba, inda Pedri ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasa mai ƙasa da shekara 23, yayin da Hansi Flick ya zama kociyan da ba kamarsa a ƙwazo a watan.
Lewandowski ya lashe ƙyautar, bayan cin Alaves ƙwallo uku rigis da zura ɗaya a ragar Seɓilla da cin Real Madrid biyu a El Clasico, kenan yana da bakwai a watan Oktoba a La Liga.
Haka kuma Lewandowski wanda ke kan ganiya a kakar nan ya ci ƙwallo uku a gasar zakarun Turai ta Champions League ta bana.
Barcelona, wadda ta yi karawa 11 a La Liga tana da maki 30 a matakin farko a teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.
Ranar Lahadi 3 ga watan Nuwamba Barcelona za ta ƙarɓi baƙuncin Espanyol a wasan mako na 12 a La Liga