Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa karuwai a Najeriya ba za su tsira daga biyan haraji ba, domin kuɗin da suke samu daga wannan sana’a ya shafi haraji a ƙarƙashin dokokin ƙasar. Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Sauye-sauyen haraji, Taiwo Oyedele, ya yi wannan bayani a wani taron wayar da kan jama’a game da haraji da aka shirya a Legas.
Oyedele ya jaddada cewa dokokin harajin Najeriya ba sa bambance tsakanin kuɗin da aka samu ta hanyar halal ko ta hanyar da ba ta dace ba. A cewarsa, duk lokacin da mutum ya yi aiki ya samu kuɗi, wajibi ne ya biya haraji. Ya ƙara da cewa kyaututtuka ko kuɗin da ake ba ‘yan uwa don kulawa ba su cikin abin da ake ɗora haraji, amma duk wata hidima da ake biyan kuɗi dole ne ta shiga tsarin haraji.
Ya ce sabon tsarin harajin da zai fara aiki daga Janairu 2026 zai sauƙaƙa tsarin haraji a ƙasar, ya rage rigingimu, ya ƙara bin doka, tare da tabbatar da adalci. A cewar sa, ma’aikatan da ke samun ƙasa da naira 800,000 a shekara za a sallame su daga harajin shiga, haka kuma ƙananan ‘yan kasuwa da ke da ƙaramin jari za su amfana da sassauci a fannoni da dama.
