‘Yan Sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan ta’adda, Akki, a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Muhammadu Dan Kani wanda aka fi sani da Akki da ya addabi hanyar Gusau zuwa Funtua.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim B. Maikaba ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau a yau Talata.

Yace, “A ranar 17 ga Satumba 2025, sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane sun kama Muhammadu Dan Kani mai shekaru 57, wanda aka fi sani da “Akki daga ƙauyen Kuraje a ƙaramar hukumar Bungudu.”

Ya kuma ƙara da cewa an kama Akki ne a garin Funtua da ke jihar Katsina, biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke alaƙanta shi da laifukan garkuwa da mutane da dama a faɗin jihar.

Abubuwan da aka ƙwato daga hannun sa sun haɗa da, bindigogi kirar gida guda 11, alburusai 25 na AK-47 harsashi 25 da kuma ƙarin harsashi guda shida.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano inda ake ƙera makaman tare da cafke wasu mambobin ƙungiyar.

Hakazalika, kwamishinan ya yi nuni da cewa jami’an ‘yan sandan da suke sintiri a kan babbar hanyar Gusau zuwa Sokoto daura da unguwar Gada Biyu a cikin garin Gusau, sun kama wasu ‘yan ta’adda guda biyu.

A cewarsa, dukkan waɗanda ake zargin an same su ne da bindigogi 18, inda ya ce a halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin a SICD Gusau.

Ya kuma ƙara da cewa rundunar da ke yaƙi da masu garkuwa da mutane ta kama Alhaji Shehu Aliyu a ƙauyen Gurusu da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum.

“An same shi da buhunan busassun ganye tabar wiwi guda 9”.

A cewar kwamishinan, Aliyu ya kasance sananne kuma mai sana’ar sayar da muggan ƙwayoyi tare da aikata laifuka sama da shekaru shida.

“A yayin gudanar da bincike wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar Tsafe, Yandato da Yanwarin Daji”. CP Maikaba ya ce.

“Wanda ake zargin ya ƙara da cewa shi mamba ne na kungiyar Kachalla Dan Goggo, kungiyar masu aikata laifuka da ta shahara wajen kitsa garkuwa da mutane a yankunan Damba, Mareri da Saminaka duk a cikin garin Gusau”.

Kwamishinan ya ce, wanda ake zargin yana hannun hukuma yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don kamo sauran mambobin ƙungiyar sa.

A cewarsa, nasarorin da rundunar ta samu na nuni da irin sauye-sauyen da ake samu da kuma ƙarin ƙwarin gwiwa a cikin rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara.

CP. Maikaba ya tabbatar wa al’ummar Zamfara cewa rundunar ‘yan sanda zata ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da ayyukan ta’addanci tare da tabbatar da tsaron lafiyar dukkan mazauna jihar.

By ukarofi