
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Laftanal Janar Theophilus Ɗanjuma (mai ritaya), ya koka game da kashe-kashen al’umma da ke faruwa a sassa daban-daban na Nijeriya.
A ƙarshen mako ne TY ya bayyana hakan a Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Takum dake Jihar Taraba, a yayin taron jinjina ga ma’aikatansa, inda ya ce lallai mahara a shirye suke da muggan makamai wajen kai farmaki ga al’umma.
Don haka ne ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya da su tashi tsaye waje kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Hakan ya biyo bayan samun rahotannin kashe-kashe ne a wasu yankunan Jihohin Benue da Filato da wasu sassan Nijeriya da ake zargin makiyaya ne suke ƙaddamar da su.
Ya kuma ce, duk da cewa a baya ya furta irin kalaman, hakan bai sa al’amarin ya ragu ba, hasali ma ƙara ƙamari ya yi, saboda haka ya ke kira ga jama’a da su ɗauki matakan kare kawunansu ganin cewa babu wanda zai kare su.
