Pafaroma ya rasu – Vatican

Spread the love

Cocin Vatican ya sanar da mutuwar shugaban majami’ar katolika ta duniya, Pafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya.

A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Pafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance sa, bayan saukar Pafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin.

Ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya, inda a baya ya shafe makonni a wani asibiti wanda aka bayyana cewa yana fama da sanyin haƙarƙari mai tsanani.

A lokacin da aka naɗa shi, ana kallon Francis a matsayin mai sassaucin ra’ayi.

Ya yi ƙoƙarin sassauta ra’ayin cocin kan abubuwan da suka shafi rabuwar aure, da auren masu jinsi ɗaya sannan kuma ya yi ƙoƙarin ganawa da jagororin wasu addinan na daban, sai dai bai yi ƙoƙarin sauya koyarwar cocin ba na asali.

Akasarin shekarun jagorancinsa, cocin ya sha suka kan zarge-zargen cin zarafin yara ta hanyar lalata, inda ya yi kira da a ɗauki matakai masu ƙwari wajen magance batun rufa-rufa, sai dai wasu na ganin cewa bai yi abin da ya dace ba wajen ganin an hukunta jagororin da suka ƙi bayar da rahoton malaman katolika da aka samu da cin zarafin yara ta hanyar ba, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji