Kayan aro ba ya rufe katara

Daga IBRAHIM YAYA

A ranar 5 ga watan Afrilun wannan shekara ne, al’ummar Sinawa suka gudanar da bikin Qingming, ɗaya daga cikin bukukuwan Sinawa masu muhimmanci. Sanin kowa ne cewa, al’ada wani ɓangare ne na rayuwar bil-Adama. Kuma Sinawa na daga cikin al’ummomi a duniya da har yanzu ba su yi watsi da al’adunsu na gargajiya ba. Wannan shi yake nuna cewa, duk al’ummar da waye, ita ce ta ke riƙe al’adunta, riƙo na haƙiƙa.

Ɗaya daga cikin al’adun wannan biki mai dadadden tarihi na tsawon sama da shekaru 2,500, shi ne tsaftace kabarin magata, inda yayin da ake tsaftace kabarin magabata, a kan ajiye abinci da furanni a gaban kabarin, a kuma zubawa kabarin sabuwar kasa, har ma a dasa bishiya a gyafensa. Daga bisani a durkusa a yiwa mamaci addu’a. A zamanin da jama’a kan shafe kwanaki biyar zuwa goma suna wannan biki na Qingming.

Al’ummar Sinawa, mutane ne masu girmama magaba, abin da ke ƙara nuna muhimmancin wannan biki. Wannan ya ƙara tabbatar da cewa, Sinawa ba su manta da al’adunsu na gado waɗanda suka gada daga kaka da kananni ba, kuma ba sa aron al’adun wasu ba.

Sai dai saboda shigowar zamani da wayewar kan al’umma, an dan samu wasu sauye-sauye a wannan al’ada, inda yanzu aka daina kona takardun kuɗi na jebu da aka saba yi a baya, saboda magance gurbata muhalli da yadda a wasu lokuta hakan ke haddasa gobara. Ana dai kona irin waɗannan takardun kuɗi na jebu ne, da fatan waɗanda suka mutun za su kasance cikin alheri da wadata.

Wani abu mai muhimmanci shi ne, lokacin Qingming lokaci ne na noma, domin a lokacin an fara dumi kana ƙasar da ta daskare ta farfaɗo, don haka, a wannan lokaci, manoma kan duƙufa kan aikin noma da fatan samun amfanin gona mai armashi a lokaci a kaka. Kana lokaci ne na yawon shakatawa.

A taƙaice dai, ya dace kowa ce al’umma ta martaba al’adunta na gargajiya, kamar yadda al’ummar Sinawa ke kiyaye duk wani nau’I na al’adunsu. Domin kayan aro aka ce ba ya rufe katara. Kuma guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni.