Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Cibiyar Kano Digital Innovation Network (KDIN) ta shirya wani taron horaswa na kwanaki biyu domin ƙarfafa sabbin kamfanonin fasaha (startups) da ƙanana da matsakaitan sana’o’i ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, ingantacciyar tsari da bunƙasa harkokin kasuwanci mai ɗorewa.
Taron mai taken “Bita, Haɗin Kai da Tsare-tsaren Aiki Domin Samar da ƙirƙire-ƙirƙire da ya Haɗa Kowa,” ya haɗa da masu kafa sabbin kamfanoni, cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a fannin domin tattauna ƙalubalen da ke addabar harkokin kasuwanci tare da samar da mafita masu amfani.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban KDIN, Abdulsalam Abdulrashid Hamza Maiturare, ya ce an tsara shirin ne domin bai wa ‘yan kasuwa ilimi da dabarun da za su taimaka musu wajen gina kasuwanci mai ɗorewa da faɗaɗawa.
Ya bayyana cewa da dama daga cikin masu sana’o’i suna shiga harkokin kasuwanci ba tare da cikakkiyar fahimta ba kan tsarin kasuwanci, muhimmancin samfuransu, kwastomomin da suke hari da kuma albarkatun da ake buƙata wajen tafiyar da kasuwanci.
A cewarsa, taron ya mayar da hankali ne wajen ilmantar da mahalarta kan yadda ake kafa kasuwanci yadda ya kamata, sarrafa shi cikin inganci da kuma hanyoyin bunƙasa sana’o’insu zuwa matakai masu girma.
Hamza Maiturare ya bayyana cewa ranar farko ta taron an buɗe shi ga jama’a, inda mahalarta suka zarce hasashen da aka yi, domin kuwa sama da mutum 120 ne suka halarta duk da cewa an tsara karɓar mutum 100 ne kacal.
Ya ƙara da cewa, rana ta biyu ta kasance ta musamman ga masu ruwa da tsaki, masu sha’awar fara kafa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire domin tsara hanyoyin aiwatar da shawarwarin da aka cimma daga tattaunawar ranar farko.
Shugaban KDIN ya jaddada cewa haɗin gwiwa da gina alaƙa tsakanin mahalarta na daga cikin manyan manufofin taron, domin samar da damar samun goyon baya da shawarwari daga ƙwararru a fannin.
Ya kuma bayyana cewa KDIN ce ta shirya taron ne tare da haɗin gwiwar Ideas Global Academy ƙarƙashin jagorancin Dakta Mustafa Shehu, Babban Sakataren na Hukumar Raya kirkire-kirkire na Jihar Katsina.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yabawa masu shirya shirin, suna mai cewa horon ya ƙara musu fahimta kan bunƙasa kasuwanci, fasahohin zamani da ƙirƙirar ingantaccen abu a kafafen sadarwa.
ɗaya daga cikin mahalarta, Samiha Abdulsalam, ta ce horon ya taimaka mata sosai wajen koyon yadda za ta yi amfani da fasahar zamani da intanet domin bunƙasa kasuwancinta na yau da kullum.
Ana sa ran wannan taro zai taimaka matuƙa wajen faɗaɗa harkokin kasuwancin fasaha a Kano ta hanyar ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, da haɗin gwiwa tsakanin sabbin ’yan kasuwa masu son bunƙasa fasaharsu.
