Kebbi: An kama ɗan Jamhuriyar Nijar da shanun da Lakurawa suka sace

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

‘Yan sandan Tarayyar Nijeriya a garin Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a yankin ƙaramar Hukumar mulki ta Arewa da ke Jihar Kebbi sun cika hannu da wani mutum mai suna Salihu Umar ɗan asalin Dogon Dutsi da ke Jamhuriyar Nijar a kasuwar Bachaka da shanu 10 da Lakurawa suka sace daga garin Zogirma da ke ƙaramar Hukumar mulki ta Bunza kimanin sati biyu da suka wuce.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta bakin jami’in hulɗa da jama’a, Sufurtanda Nafi’u Abubakar ya ce, yanzu haka dai ‘yan sanda suna nan sun baza komarsu, don farauto sauran ɓarayin yayin da bincike ke gudana a ofishin jami’an ‘yan sandan ciki da ke Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar ta Kebbi.

A wata mai kama da wannan, haka-zalika, ranar Talatar da ta gabata waɗansu mutane da a ke kyautata zaton Lakurawa ne sun shiga garin Gulma, inda suka yi gaba da shanu da aka ce sama da 150 ne, sai dai Gwamna Malam Nasir Idris na Jihar Kebbi bai yi ƙasa a gwiwa ba, inda bayan samun rahoton nan da nan ya sanar da jami’an tsaro, su kuma suka bi su.

Malam Hussaini ɗaya daga cikin ‘yan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace wa shanun ya bayyana cewa, shanun ba na mutum ɗaya ba ne kuma sun kai kimanin 150. Sai dai jami’an tsaro da suka bi sawun ɓarayin sun samu nasarar dawo da waɗansu daga cikinsu.

Haka-zalika bayanai daga ƙaramar Hukumar Augie da ke jihar ta Kebbi sun nuna cewa, a jiya Alhamis waɗansu da a ke sa ran ɓarayin daji ne sun kai wa hakimin ƙauyen Diboni hari, inda suka sare shi a hannu, amma a nan ma dai jami’an tsaro da ’yan sa-kai da ke aiki a wannan yankin sun fatattake su ba tare da sun kashe kowa ba ko ɗaukar wani mutum ko dabbobi, ba kamar yadda wani ma’aikacin lafiya da ke aiki a wani ƙaramin asibiti da ke yankin da ya sha da ƙyar a hannun Fulanin ba.

Shugaban ƙaramar Hukumar Argungu, Hon. Aliyu Sani Gulma, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa yadda ya ke bai wa sha’anin tsaro muhimmanci, saboda a duk lokacin da ya kira shi ya kan ɗauki mataki cikin lokaci. Ya kuma yi kira ga al’umma da su riƙa shaida wa jami’an tsaro da ke kusa da su a duk lokacin da suka ga wani abu da ba su yarda da shi ba.

By ukarofi