Ni ne na ba Nafisa kyautar N200,000, ba daga Gwamnatin Tarayya ba – Ministan Ilimi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Nijeriya ta yi ƙarin haske kan cece-kuce dangane da kyautar kuɗi da aka baiwa ɗaliban Nujeriya da suka yi nasara a gasar duniya ta TeenEagle 2024/2025 da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.

Bayanin ya biyo bayan rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da ke nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta bada Naira Miliyan 1.7 a matsayin kyautar kuɗi ga haziƙan matasan.

A watan Agusta 2025, an ba da N200,000 ga Nafisa Abdullahi, wacce ta lashe gasar Turanci ta duniya ta TeenEagle. Jim kaɗan bayan wata jarida ta yanar gizo ta ruwaito cewa Muhammad Manga, shugaban kamfanin Manga Automobiles, ya baiwa Nafisa Abdullahi Aminu kyautar kuɗi N800,000, wacce ta lashe gasar Turanci ta TeenEagle ta duniya.

Ya zuwa ranar 29 ga Agusta, 2025, an bayar da rahoton cewa, an bayar da jimillar kuɗaɗen da aka ware wa waɗanda suka yi nasara a Nijeriya ya kai Naira miliyan 1.7.

Ma’aikatar ilimi ta fayyace gaskiya a shafinta na ɗ domin cirewa mutane shakku kan kyautar da ake cewa gwamnatin tarayya ta ba bayar.

Ma’aikatar ta ce, abin takaici ne yadda ake ta yada cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ba da kyautar N200,000 ga Nafisa.

Sanarwar ta ce, labarin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne saboda kyautar ba daga hannun Bola Tinubu ta fito ba.

Ma’aikatar ta ce, hakan na daga cikin ƙoƙarin minista, Tunji Alausa ne domin ƙara wa ɗalibar watau Nafisa da sauran ɗalibai ƙarfin gwiwa.

Sanarwar ta ce, “Ma’aikatar ilimi ta ci karo da wani rahoto da ake yadawa kan kuɗin da aka ba ɗaliban da suka yi nasara a gasar Turanci a London.

“Saboda cire shakku, Ma’aikatar tana mai tabbatar da cewa kyautar da aka ba ɗaliban a ranar 28 ga watan Agustan 2025 kyauta ce daga ministan ilimi, Tunde Alausa.

“Wannan kyauta ba daga gwamnatin tarayya ba ce ko kuma ma’aikatar ilimi da kanta, wanda kuma an sanar a ranar ba da kyautar.”

Ma’aikatar ilimi ta ce, ya kamata al’umma su sani babu wani kasafi da aka ware mata domin ba da kyaututtuka ko karrama ’yan Nijeriya.

Ta ce, kuɗin da ake warewa ma’aikatar an tanade su ne domin bunƙasa harkokin ilimi kamar yadda tsare-tsaren gwamnati su ke.

Mutane da dama sun nuna rashin jin daɗi kan kyautar wanda aka ce gwamnatin tarayya ne ta bayar kafin ma’aikatar ilimi ta yi ƙarin haske.

By ukarofi