Kira ga matasa a kan bangar siyasa

A yanzu haka an buga kugen siyasa, masu neman ƙuri’un jama’a za su fara bazama neman goyon bayansu da kuma ƙuri’unsu. A irin wannan lokacin ne ’yan siyasa suke amfani da matasa domin jan hankalin jama’a su zaɓe su da kuma yin barazana ga waɗanda suka tabbatar ba za su zaɓe su.

A duniyar dimokuraɗiyya kuma (musamman a Nijeriya) babu abin da ’yan siyasa suke amfani da shi wajan yaudarar al’umma a wannan zamani face sai sun danganta shi da rayuwar matasa, kasancewar babu wani buri da matasa suke buƙata face suga sun tsinci rayuwarsu cikin sauƙi da samun ingancin rayuwa ta hanyar dogaro da kai.

Wajan neman saukin rayuwar ne ake durmiyar da mafi yawan su ta hanyar kwaɗayi da gaggawar samun jin daɗin da shi ne musabbabin taɓarɓarewar rayuwarsu da samun damar wasu ’yan siyasa zuwa ga gurɓata musu rayuwarsu cikin sauƙi; wajen amfani da su domin cin zarafin al’umma da ba su tallar ƙarya da tarbiyyar rashin kishin kai da kuma dagula musu rayuwa.

Da wannan nake nake kira ga ’yan uwana matasa, da mu hankalto, mu tuna da iyayenmu da malumanmu da gidajenmu ne a kewaye da mu, hasali babu mai son mahaifansa da ‘yan uwansa su shiga cikin ƙuncin rayuwa ko halin wai ni ’ya su, in kuwa hakane, to ya kamata mu shiga taitayinmu wajan yaƙar miyagun ɗabi’un da muka aro daga dimokradiya mu kawo zaman lafiya da cigaban al’umma ta hanyar zaɓen shuwagabanni nagari waɗanda ke da burin ganin mun zama manyan gobe.

Siyasa na da mahimmanci a kowacce ƙasa ta duniya da ke bin tafarkin demokraɗiyya. Dalili kuwa shi ne, siyasa tsarin demokraɗiyya ce da ta baiwa jama’a damar zavan waɗanda suke ganin sun dace da su, waɗanda za su biya musu buƙatunsu da kuma share musu hawaye.

Jama’a kan ba da goyon baya ga waɗanda suka yi imanin za su wakilce su kuma wakilci nagari ba waɗanda za su je don wakiltar kansu ba.

Ta ya ya jama’a ya kamata su tabbatar da cewa sun zaɓi shuwagabanni nagari ba zaɓen tumun dare ba? Akwai muqala (rubutu) da muka yi ni da ɗan’uwa Aliyu Samba akan su waye suka cancanta mu zaɓa a wannan shekarar ta 2023, za ku iya nema a jaridu ko kuma yanar gizo ku karanta domin jin waɗanda ya kamata mu zaɓa a 2023, amma yanzu ina so ne nayi kira ga ‘yan uwana matasa akan bangar siyasa.

Tun bayan komawarmu tsarin demokraɗiyya yau kimanin kusan shekaru Ashirin da huɗu (24) ke nan, ‘yan siyasar ƙasar ke amfani da mu (matasa) domin cim ma manufofinsu na siyasa. Ba laifi ba ne ‘yan siyasa su nemi goyon bayan mu. Abin da yake laifi, shi ne, amfani da mu da suke a matsayin ‘yan bangar siyasa domin samun nasara a zaɓe.

A zaɓukan da suka wakana a baya, ’yan siyasa a Nijeriya suna ba mu kuɗi mu kuma sai mu sayi ƙwaya da sauran ababen sa maye da makamai muna bi muna razanar da abokan hamayyarsu da sauran jama’a.

A wasu lokutan mukan yi fito-na-fito tsakanin mu ‘yan bangar siyasa da wasu abokanmu ’yan bangar siyasar daban. Wani lokaci mu ji munanan raunuka, a wasu lokuta kuma mu rasa rayuka. Wannan abin takaici da me ya yi kama? Shin mu da muke bari ana amfani da mu domin cim ma manufar zaɓe duk da cewa mun san ’yan siyasa za su yi watsi da mu da zarar sun yi nasara mun san ciwon kan mu kuwa?

Muna da masaniya akan cewa ’yan siyasar nan ba su da mu da mu ba illa kawai sun mai da mu tamkar matattakala ce da suke takawa domin cin zaɓe ko ta halin ƙaƙa? Amsar da nake so samu, ita ce, ta ya ya mu matasa za mu jajirce mu ƙi yarda ana amfani da mu a matsayin ‘yan bangar siyasa ana ba mu wasu ’yan kuɗaɗe ƙalilan da ba za su taimaka mana idan muka kai kanmu ko aka kai mu asibiti ba?

Kuma ba za su ciyar da mu da iyalanma har na tsawon shekara huɗu ba! Sannan mu dawo ana mana kallon marasa mutunci da tunani. Lamarin da kan iya sanadiyyar hasarar rayukanmu da ci bayan ƙasarmu.

Tabbas muna da muhimmancin gaske a cikin kowacce al’umma, tasirinmu yafi gaban a zura mana idanu muna gudanar da rayuwa yadda muke so. Wajibi ne da ya hau kan al’umma da gwamnati su yi tattalin rayuwarmu, su samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau gare nu domin mu siffantu da su, haka kuma a yi mana bayanin illolin abubuwa marasa kyau don mu ƙaurace musu.

Duk wata ƙasa da ta cigaba a wannan duniyar, idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan cigaban, za a ga a hannun matasansu ya ke. Saboda ba su yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba.

Haƙƙi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye da su kasance mataki na farko ta inda ’ya’yansu za su koyi tarbiyya da mu’amala da mutane da kiyaye dokokin ƙasa da oda da ƙaurace wa ayyukan ɓarna da sauransu.

Idan iyaye suka gaza aikata hakan ga ’ya’yansu, babu tantama a daidai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (matashi) ya fara mu’amala da wasu abokai a waje, za su koya masa dukan ɗabi’un da suka ga dama.

A wasu lokutan ma ba sai sun koya masa ba, yanayin mu’amalan da ke tsakaninsa da su ne zai sa ya riqa kwaikwaiyon yadda suke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina tasa ɗabi’ar.

Shekaru sun shuɗe muna ta addu’ar Allah ya kawo mana shuwagabanni nagari a ƙasarmu. Shekaru a baya iyayenmu suna ta cewa mune manyan gobe, mu ne magani ƙasa, amma ga shi har yanzu mun kasa zama manyan goben, balle mu gina ƙasar. Shin me ya janyo haka? Me ya sa har yanzu ƙasarmu ta kasa zama yadda muke mata fata kuma muke mata addu’a?

Amsar a nan ita ce, mu matasa mun kasa fahimtar irin gudumawar da za mu iya bayarwa domin ƙasarmu ta gyaru. Mun yi shiru mun kasa cewa uffan kan yadda ɓarayi ke ta kwashe dukiyoyin ƙasarmu, mun yi shiru mun kasa haɗuwa wurin guda domin mu tabbatar da mun haɗa kai mun gyara ƙasarmu.

Ba komai ba ne yake sani takaici illa yadda muka yi sakaci da harkar ilmi. Ga mu da yawan gaske, amma ba mu da aikin yi sai kallon ƙwallo da taɗin ƙwallo da kuma yawon bangar siyasa. Ga mu da yawan amma mun ƙi yarda mu nemi ilimi domin mu tallafa wa ƙasarmu. Wannan shi ne dalilin da ya sa baragurbin ’yan siyasa waɗanda ba burinsu ganin cigaban Nijeriya ba suke amfani da mu wurin cim ma mummunar manufarsu ta aika-aika.

Su ne suke ba mu makamai da ƙwaya domin mu aikata abubuwan da suke so. Don haka matasa mu farka, mu tashi mu nemi ilimi, kuma mu ƙaurace wa bangar siyasa, domin rayuwarmu tana da amfani ga al’umma.

A ƙarshe ina ƙara kira ga iyayye da sauran al’umma da su tashi tsaye wajen yi wa matasa da ƙasarmu Nijeriya addu’a. Allah Ya datar da mu, ya ba mu shuwagabanni nagari.

MOHAMMED BALA GARBA ke muku fatan alheri. 08098331260.