Kisan Edo: Ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua ta yi allawadai

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar haɗin kan yankin Funtua kwamared Mansir Suleiman yayi Allah wadai da kisan gillar da akai wa mutane 16 yan asalin Jihar Kano a Jihar Edo.

A wata takarda ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar,ya nuna takaicin sa da damuwa yadda aka kashe waɗannan mutane da suke kan hanyar ta komawa Jihar Kano.

Ya bayyana cewa yan Arewacin ƙasan da sauran jama’ar Nijeriya ba za su zura ido wasu miyagun mutanen na ɗaukar doka a hannun su.

Kwamred Suleiman sai yayi kira ga gwamnonin Arewa, jami’an tsaro da gwamnatin tarayya da su tabbatar an zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci kuma ai masu hukunci mai tsanani.

“Babu wata gwamnatin a duniya da tasan abinda take yi za ta sa ido irin waɗannan ɓata gari na aikata irin wannan ɓarnar ta kyale su”inji shugaban ƙungiyar.

“Domin haka dole ne doka tayi aikin ta a nan domin ya zama darasi ga masu irin wannan hali”kwamred Suleiman ya ce.

Daga nan sai ya miƙa ta’aziyar sa a madadin ƙungiyar da gwamnatin da al’ummar Jihar Kano bisa wannan rashi da suka yi.

Su dai wannan da suka rasa rayukansu mafarauta ne da suka fito daga Jihar Ribas suka biyo hanya ta garin Orume ta Jihar Edo Kan hanyar su ta komawa gida Jihar Kano.

By ukarofi