Daga AISHA ASAS
A ‘yan kwanakin nan ne aka samu musayar yawu tsakanin ma’abota kallon finafai inda taƙadama kan furucin daraktan shahararren fim ɗin Hausa da ya samu karuwa a duniya, mai suna ‘Mai Martaba’ wanda ya lashe lambar yabo ta Academy Awards, ta arke kan furucin daraktan na cewa, masana’antar Kannywood da Nollywood sun ƙi shi saboda addininsa da yankinsa.
Wasu waɗanda suka kasance masoya ga daraktan sun musunta maganar inda suke ƙoƙarin kare gwanin nasu, yayin da waɗansu ke ƙoƙarin tabbatar da zancen.
Daraktan fim ɗin ‘Mai Martaba’, Prince Daniel, fito ya musanta kalaman da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai na cewa, Kannywood da Nollywood sun ƙi shi saboda addininsa da yankinsa.
Fim ɗin ‘Mai Martaba’ ne Najeriya ta shiga gasar Oscar na bana, wanda kwamitin da aka zaa a hukumance na Najeriya ya zaa a angaren mafi kyawun finafinai na ƙasa da ƙasa da lambar yabo ta Academy.
Da yake mayar da martani ga rahotannin kafafen yaɗa labarai, daraktan ya ce, bai taa yin wata hira da ya yi irin wannan iƙirarin ba.
Rahotannin, inji shi, da alama sun samo asali ne daga wata mummunar fassara da aka yi wa kalaman nasa yayin wani taron baya-bayan nan a birnin Los Angeles na Jihar California.
Daniel, wanda aka fi sani da Aboki, ya ce: “An janyo hankalina ga wasu wallafe-wallafe da kanun labarai da ke nuni da cewa, Kannywood ta ƙi amincewa da ni saboda addinina. Da kuma Nollywood saboda yankina. Maganar gaskiya ban yi wata hira da wata jarida ba dangane wannan batu.”
A cewarsa, a yayin taron tambayoyi da amsa a taron Nollywood A Hollywood a farkon watan nan a birnin Los Angeles, ya tattauna ƙalubalen da ya fuskanta yayin ɗaukar shirin ‘Mai Martaba’ da kuma yadda ya sami kansa a gasar Oscar.
Daga cikin matsalolin da ya ambata akwai matsalar tsaro a lokacin da ake yin fim a Arewa maso Yamma da kuma matsalolin kuɗi, musamman a matsayinsa na sabon darakta da ke aiki tare da masu tasowa.
Ya ce, a yayin wannan tattaunawa, ya bayyana yadda masana’antar ta kasance kamar ta rabu cikin fahimtarsa da aikinsa.
“Wani lokaci angaren masana’antar Kannywood kamar yadda suke kallon mu a matsayin Nollywood, suma Nollywood suna ganin mu a matsayin Kannywood, don kawai ni ɗan Arewa ne,” inji Daniel, ya ƙara da cewa, an yi masa mummunar fassara.
“An yi wannan bayanin ne da kyakkyawar niyya, don bayyanin da zai sa masu sauraro a cikin wurin su fahimci yadda masana’antar ta ke a Najeriya da kuma irin ƙalubalen da aka fuskanta.”
Ya ƙara jaddada alaƙarsa da Kannywood, inda ya ce, “Na yi imanin cewa, wannan tsokaci ba a fahimce shi sosai ba, domin a bayyane yake cewa, Kannywood ba ta taa ƙi na bisa ƙabilanci ko addini ba, a maimakon haka ta kasance wani tubali na goyon baya a matsayina na mai shirya finafinai.”
Daraktan wanda ya lashe lambar yabo ya kuma bayyana irin gagarumin goyon bayan da ya samu daga masu kallo a lokacin da yake haska finafinansa a sinima da kuma samun goyon bayan ƙwararrun masana a masana’antar har ma da masu tasowa.
Ya ƙara da cewa: “Zan faɗa da babbar murya cewa ni ɗan fim ɗin Najeriya ne, duk da cewa na fito ne daga Arewa, ina zaune ne a Kano, inda nake yin sana’ata da ta kai ne zuwa Kannywood. Na samu goyon baya mai yawa a masana’antar ba tare da nuna ƙyama ba.”
Daniel ya jaddada ƙudurinsa na bunƙasa masana’antar da kuma canza irin kallon da ake yi wa Arewa, ya ƙara da cewa, “Za ci gaba da yin aiki tare da takwarorina da kuma iyayen da suka kafa Kannywood domin ɗaukaka matsayin masana’antarmu ta hanyar ba da labaranmu ga duniya, da samar da guraben aikin yi ga matasanmu, tare da sauya akalar labaran Arewa na irin kallon da ake yi mana da ke da nasaba da ta’addanci.”
Saidai jim kaɗan bayan wannan furuci ne aka samu wanzuwar wani faifan bidiyo da ke nuni da daraktan ya yi amai ne ya yi ƙoƙarin lashewa.
Wani faifan bidiyo wanda Mujallar Fim ta fitar a daren ranar ya nuna inda daraktan Najeriya Prince Daniel ke furta cewa, masana’antar Kannywood da Nollywood sun ƙi shi a farkon fara harkar fim saboda addininsa da yankinsa.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da daraktan ‘Mai Martaba’, wanda ya lashe lambar yabo ta Najeriya a hukumance a gasar Academy Awards na bana, ya fitar da kakkausar martani kan lamarin.
Da yake mayar da martani, daraktan ya jaddada cewa kalaman da ya yi a ƙasar Amurka na da nasaba da rabe-raben masana’antar finafinan Najeriya tsakanin Kannywood (Arewa) da Nollywood (Kudu).
Sai dai a cikin faifan bidiyon da Mujallar Fim ta samu, an ga Daniel, wanda aka fi sani da Aboki, ana hira da shi kan fitaccen fim ɗinsa a wani angare na bikin finafinai na “Nollywood a Hollywood” da aka gudanar a farkon watan nan a birnin Los Angeles na Jihar California ta Amurka.
Da aka tambaye shi a gaban mahalarta taron ya bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake shirya fim ɗinsa a Arewacin Najeriya, daraktan wanda ya fito daga Arewa maso Gabas ya amsa da cewa:
“Eh to, da yawa. Na taa faɗar cewa, a matsayina na ɗan fim na haɗu da ƙalubale a lokacin wannan shiri, na shiga tsaka mai wuya, saboda ni ɗan Arewa ne, Arewacin Najeriya, amma ni Kirista ne, kuma Kannywood masana’anta ce da galibin su Musulmai ne. Kuma angaren Nollywood na masana’antar Kiristoci ce. Don haka, na shiga cikin tsaka mai wuya, sakamakon wani lokaci Kannywood ba ta yarda da ni ba saboda addini, kuma Nollywood ba ta yarda da ni ba saboda ina ɗan Arewa.
“Saboda haka, wannan angare na kallona a matsayin Kirista mai yin fim a masana’antar Kannywood, sannan kuma ɗaya ɓangaren suna kallona a matsayin ɗan Arewa mai sana’a a Nollywood. Saidai hakan ta canza zane a yanzu da aka zaɓi fim ɗin ‘Mai Martaba’ a matsayin mai wakiltar Najeriya a gasar Oscar ta bana.”
Faifan bidiyon, wanda ake samu a YouTube, na ɗauke da ainihin abin da Prince Daniel ya faɗa kamar yadda wasu jaridu na kafafen sadarwa na Najeriya suka buga, ciki har da Pulse da New Citizen.
