
Daga BELLO A. BABAJI
Gwmanan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya umarci a dakatar da baki ɗaya haramtattun ƙungiyoyin ƴan bijilante da ke gudanar da harkokinsu a jihar.
Ya kuma dakatar da kwamandan jami’an tsaro na jihar, CP Friday Ibadin (mai ritaya).
A wata takarda da Sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne biyo bayan iftila’in da ya faru a garin Uromi na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa a jihar, inda aka kashe wasu matafiya ƴan Arewa guda 16 a ranar Alhamis.
Ya ce, jami’an ƴan bijilante da suka jagoranci kisan matafiyan a ranar 27 ga watan Maris, suna aiki ne ba tare da an masu rajista da hukumar tsaro ta jihar ba, wato Edo State Security Corps, ya na mai cewa aikin nasu ya saɓa wa tsarin gwamnatin Okpebholo da dokokin jami’ai a jihar.
Ya kuma ce, kawo yanzu an kama mutane 14 da ake zargin su da hannu a laifin yayin da kuma ake cigaba da farauto sauran masu laifin ƙarƙashin jagorancin tawagar da Sufeton ƴan sanda ya naɗa.
Kazalika, ya ce gwamantin ta yarda da cewa dokar ƙasa ta sahalewa kowane ɗan ƙasa ya yi zirga-zirga a kowane ɓangare na ƙasa da gudanar da harkokinsa ba tare da muzgunawa ba.
Kazalika, gwamnatin jihar ta ba tare da iyalan mamatan da kuma gwamantin jihar Kano a yayin alhinin rashin kasancewar galibin su ƴan Kano ne.
