
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alla-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta da ke kan tafiya da wasu ƴan bijilante a garin Uromin na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa dake Jihar Edo suka tsare su.
Shugaban ƙasar ya bayyana kaɗuwarsa game da iftila’in na ranar Alhamis, lamarin da ya sa ya umarci ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi tare da zaƙulo waɗanda ke da hannu a ciki da hukunta su.
Ya kuma jajenta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa tare da tabbatar masu da cewa, ba za a bari wasu mujirimai su zubar da jinanan ƴan Nijeriyar da ba su ji ba, ba su gani ba, kamar yadda Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda, ranar Juma’a.
Ya ce, irin wannan ɗaukar doka a hannu ba zai taɓa samun gurbi a Nijeriya ba, don haka ɗan Nijeriya ya na da ƴancin zuwa ko’ina a ƙasar.
Kazalika, ya yaba wa Gwamna Monday Okpebholo na jihar da manyan yankin da abin ya faru wajen ƙoƙarin kwantar da tarzoma acikin al’umma.
